Wasu daga cikin mutanen sun ce matansu sun karbo bashi domin samun kuɗin abinci a gida, yayin da su kuma suke jiran a biya su kuɗin da aka yi musu alkawari.
A karkashin dokar Taiwan, daukar ko yada bayanan sirri ko ayyukan mutum ba tare da sanar da shi ba na iya janyo hukuncin daurin shekara uku a gidan yari da kuma tarar NT$300,000.
Binciken gawarsa da aka gudanar daga baya a Birtaniya ya gano wasu ƙwayoyin halitta a cikin huhunsa da suka yi daidai da hyaluronic acid da aka yi amfani da shi wajen aikin.
A cewarsa, waɗanda aka kama sun ƙunshi mata 10 da maza 12, kuma wasu daga cikinsu sun amsa cewa suna gudanar da ayyukan kawalci wato “hook-up”, tare da yin amfani da miyagun ƙwayoyi.
Ya ambaci calcium carbide a matsayin wani sinadari da ake amfani da shi wajen tilasta wasu 'ya'yan itatuwa, kamar ayaba, mangwaro, gwanda da tumatir, su nuna cikin gaggawa.
Yan Kudancin Kaduna, a tsawon shekarun da Honourable Christopher Musa ya kwashe yana aikin soja, wane irin ci gaba ya kawo muku da za ku iya dubawa a yau ku ce: “Eh, wannan mutum ya nuna mana ƙauna da gaske”?
Ya kuma danganta matsalar tsaro da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, yana cewa manoma da dama ba sa iya zuwa gonakinsu saboda rashin tsaro, lamarin da ya shafi samar da abinci.
“A ƙarƙashin wannan gwamnati, za ku iya zagin Shugaban ƙasa, ku kai masa hari da kalamai, sannan ku koma ku kwanta ba tare da an kwankwasa ƙofarku da tsakar dare ba,” in ji Tinubu.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.