Kotu ta ɗaure magidanci bayan ya yi amfani da ɓoyayyar kyamara wajen kama matarsa tana cin amanarsa
Daga Wakiliya
Wani mutum a Taiwan ya samu kansa a gidan yari na tsawon watanni biyar bayan da ya dauki bidiyon matarsa tana cin amanar aure da wani mutum, ta hanyar amfani da wata ɓoyayyar kyamara mai sarrafa kanta.
Rahotannin kafafen yada labarai na Taiwan sun ce mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya gano abin da ke faruwa ne bayan da ya fara zargin matarsa da rashin gaskiya.
Ma’auratan sun yi aure ne a shekarar 2021, inda suka koma gidan iyayen mutumin. Haka kuma suna da wani gida da suke zuwa lokutan hutu.
A wani lokaci da suka je gidan, mutumin ya lura da wata buroshin hakori da bai san daga inda ta fito ba. Hakan ya kara masa shakku.
Daga bisani ya duba hotunan kyamarar filin ajiye motoci, inda ya ga wani mutum da ya taba kai matarsa gida daga wurin aiki.
Da ya tambayi matarsa, ta musanta cewa akwai wata alaka tsakaninta da mutumin, kuma mijin ya yarda da bayaninta.
Sai dai bayan watanni uku, ya gano cewa zargin da yake yi haka din ne.
Yadda robot vacuum ya tona asirin
A lokacin da suke gidan hutun, mutumin ya kunna wata na’urar robot vacuum daga nesa ta manhajar wayarsa.
Mijin ya kunna na’urar da nufin yi wa matar tasa ba zatan soyayya “suprise” tunda ya san ta je gidan shakatawar nasu.
Sai dai maimakon abin da yake tsammani, kwatsam sai ya ga matarsa tare da wani mutum a cikin gidan suna lalata.
Maimakon ya shiga gidan nan take, ya ci gaba da daukar hotunan bidiyon domin amfani da su a matsayin shaida a kotu.
Daga bisani ya kai matarsa da mutumin kotu, yana neman diyya ta NT$2m, wato kusan dala 68,000, bisa zargin cin amanar aure.
Kotun ta yanke cewa alakar matar da mutumin ta wuce iyakar abota, inda ta umarce su da su biya mutumin NT$500,000 a matsayin diyya.
Amma shi ma ya fuskanci shari’a
Duk da nasarar da ya samu a shari’ar farko, matar itama ta kai shi kara kan yadda ya dauki hotunansu ba tare da izininsu ba.
Kotun ta ce ko da yake bidiyon ya taimaka wajen tabbatar da cin amanar aure, hakan bai ba shi damar kutsawa cikin sirrin mutanen da aka dauka a bidiyon ba.
A karkashin dokar Taiwan, daukar ko yada bayanan sirri ko ayyukan mutum ba tare da sanar da shi ba na iya janyo hukuncin daurin shekara uku a gidan yari da kuma tarar NT$300,000.
A wannan shari’ar, kotu ta yanke wa mijin hukuncin watanni biyar a gidan yari, tare da biyan tarar NT$150,000.
Lamarin ya jawo hankali saboda yadda mutumin ya yi amfani da na’urar robot vacuum wajen gano cin amanar matarsa, amma daga bisani irin wannan shaida ta zama dalilin da ya sa shi ma aka gurfanar da shi a gaban kotu.




