“Sau Uku muna gayyatar ta ba ta zo ba bata turo wakili ba amma ta je bikin Lagos” – Sarauniyar bikin al’adun ABU ta soki Hannatu Musawa
Daga Wakiliya
Sarauniyar bikin al’adun gargajiya ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Suwaiba Abdulkarim, ta bayyana takaicinta kan yadda Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Zamani, Hajiya Hannatu Musawa, ta kasa halartar bikin jami’ar duk da cewa an gayyace ta sau uku.
Suwaiba ta ce ɗaliban jami’ar sun kai wa ministar wasiƙar gayyata har ofishinta da ke Abuja, amma duk da haka ba ta samu halartar bikin ba, ko kuma ta tura wakili.
Ta yi waɗannan kalamai ne a wata hira da RFI Hausa, inda ta ce abin ya ba ta takaici musamman bayan da ta ga ministar ta halarci bikin al’adu da aka gudanar a Legas.
“Mun gayyaci Ministar Al’adu Hajiya Hannatu sau uku, amma ba ta zo ba. Sai muka ga ta halarci bikin da aka yi a Legas. Gaskiya abin ya yi mana ciwo kuma ya ba mu takaici,” in ji ta.
Ta ce ɗaliban ABU sun kashe kuɗinsu wajen kai wasiƙar gayyatar, amma ba su samu gamsasshiyar ba.
A cewarta, wannan ba matsala ce da ta shafi ministar kaɗai ba, domin tana ganin ana samun ƙarancin kulawa ga wasu shirye-shiryen al’adu daga Arewa.
“Muna yin abubuwa amma saƙonmu ba ya isa”
Sarauniyar ta ce tana ganin al’adun Arewa ba sa samun irin tallafin da kuma kulawar da ake bai wa irin waɗannan abubuwa a wasu sassan ƙasar.
“Mu a Arewa muna yin abubuwa, amma saƙonmu ba ya isa inda ya kamata. Idan aka yi irin wannan abu a wasu wurare, nan take za ka ga an karɓe shi kuma an ba shi muhimmanci,” in ji ta.
Ta kuma ce akwai bambanci tsakanin yadda ake kallon sarauniyar bikin al’adu a wasu jami’o’in kudancin Najeriya da kuma yadda ake kallon waɗanda ke Arewa.
A cewarta, bayan ɗaliba ta kashe kuɗi wajen sayen fom, biyan kuɗin taken sarauniya da shirya kayayyakin bikin, ba kasafai take samun wata dama ko tallafi bayan kammala bikin ba.
Ta kawo misalin Jami’ar Legas, inda ta ce sarauniyar bikin al’adun jami’ar na iya samun damar shiga wasu shirye-shiryen gwamnati da na kamfanoni a tsawon shekarar.
Ta ce tana fatan a samu irin wannan kulawar ga matasan da ke tallata al’adun Arewa.




