Dan Najeriya ya mutu bayan aikin ƙara girman mazakuta a Thailand

DA DUMI-DUMI

Dan Najeriya ya mutu bayan aikin ƙara girman mazakuta a Thailand

Daga Wakiliya

Wani attajirin ɗan kasuwa kuma fitacce a kafafen sada zumunta ɗan asalin Najeriya, Igho “Tiny” Ubiribo, wanda aka fi sani da Denisi ko Ego, ya rasu yana da shekaru 43 bayan ya yi wani aikin ƙara girman mazaƙutarsa a ƙasar Thailand.

Rahotanni sun ce Igho ya je Thailand tare da matarsa, Danielle Simba Allen, domin yawon buɗe ido, inda a watan Maris aka yi masa allurar hyaluronic acid da lidocaine mai nauyin mililita 40 a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Bayan aikin, shi da matarsa sun koma otal ɗin Marriott da ke Bangkok domin yin tausa.

Sai dai daga bisani Igho ya fara korafin ciwon ƙirji, sannan ya faɗi har sau biyu, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibitin Sukhumvit.

Da farko yana cikin hayyacinsa, amma daga baya ya sume kafin a yi masa gwajin CT scan da likitoci suka ba da shawara.

Likitoci sun gano cewa yana fama da pulmonary embolism, wato toshewar wata jijiya a huhu sakamakon gudan jini ko wani abu da ya shiga jijiyoyin jinin.

An kai shi sashen kula da marasa lafiya na gaggawa, inda ma’aikatan lafiya suka yi ƙoƙarin farfaɗo da shi ta hanyar CPR na tsawon sama da mintuna 100.

Sai dai Igho ya rasu a farkon safiyar ranar 6 ga Maris.

Binciken gawarsa da aka gudanar daga baya a Birtaniya ya gano wasu ƙwayoyin halitta a cikin huhunsa da suka yi daidai da hyaluronic acid da aka yi amfani da shi wajen aikin.

A zaman binciken dalilin mutuwarsa a Inner West London Coroners’ Court, Coroner Jean Harkin ta yanke cewa aikin gyaran jikin da aka yi masa ne ya haddasa pulmonary embolism ɗin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Lamarin ya sake jawo hankali kan haɗarin da ka iya tattare da wasu nau’o’in ayyukan gyaran jiki, musamman idan aka yi su a wuraren da ba a san cikakken tarihi ko ƙa’idojin lafiyarsu ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img