X (Twitter) ta soke tsarin biya na Revenue Sharing, ta ƙaddamar da sabon tsarin biyan na Original Content Rewards

X ta soke tsarin rabon kuɗaɗen shiga, ta ƙaddamar da sabon tsarin biyan masu ƙirƙirar abun ciki

Daga Wakiliya

Kamfanin X ya sanar da dakatar da tsarin Revenue Sharing da yake bai wa masu ƙirƙira damar samun kuɗi daga abubuwan da suke wallafawa a dandalin.

Kamfanin ya ce zai maye gurbin tsarin da sabon shirin Original Content Rewards, wanda zai mayar da hankali wajen bai wa masu ƙirƙirar abubuwan na asali lada.

X ta ce daga ranar Juma’a ba za ta sake karɓar sabbin masu shiga tsarin Revenue Sharing ba, yayin da waɗanda suke cikinsa za su ci gaba da samun kuɗaɗen da suka tara har zuwa 7 ga Satumba, 2026.

Kamfanin ya ce za a biya tsofaffin mahalarta kuɗaɗensu na ƙarshe sau uku, inda za a fara biyan wani kaso a 14 ga Agusta, sannan a sake biya a 28 ga Agusta, yayin da kuɗin da aka samu har zuwa 7 ga Satumba za a biya su kusan 11 ga Satumba.

Daga 8 ga Satumba, masu amfani da suka cika sharuddan za su fara samun damar neman shiga sabon shirin Original Content Rewards.

Waɗanne abubuwa ne za su cancanci samun kuɗi?

A sabon tsarin, X za ta rika biyan masu ƙirƙirar abun bisa adadin qualified impressions, wato kallon abubuwan da suka wallafa daga masu amfani da ke da Premium a shafin Home Timeline.

X ta ce za a yi biyan kuɗaɗen ne duk bayan makonni biyu.

Daga cikin abubuwan da za su iya cancanta akwai bidiyo, rubuce-rubuce, barkwanci, zane-zane, rahotanni, nazari, sharhi da sauran abubuwan da mutum ya ƙirƙira da kansa.

Sai dai kamfanin ya ce sake wallafa abin da wani ya ƙirƙira kawai ba zai isa ba. Za a bukaci mutum ya ƙara nasa bayani, sharhi, nazari, barkwanci ko wata hanya ta sauya wa abin ma'ana.

X ta kuma ce sauye-sauye kaɗan kamar yanke hoto, ƙara filter, iyaka, watermark, sauya saurin bidiyo ko ƙara rubutu kaɗan ba za a ɗauke su a matsayin Original ba.

Waɗanne ne sharuddan shiga shirin?

X ta ce mai son shiga shirin dole ne ya kasance:

  • Ya kai shekara 18 ko fiye;

  • Yana zaune a ƙasar da shirin yake aiki;

  • Asusunsa yana cikin yanayi mai kyau;

  • Yana da X Premium, Premium+ ko Premium Business;

  • Yana da aƙalla verified followers 500;

  • Ya samu aƙalla 500,000 Home Timeline impressions daga verified users cikin kwanaki 90 da suka gabata.

Kamfanin ya kuma ce masu shiga shirin dole ne su riƙa wallafa abubuwan da suka ƙirƙira da kansu akai-akai.

X ta ce za a iya dakatar da asusun da ya karya ƙa'idojin shirin na ɗan lokaci ko kuma a cire shi gaba ɗaya, gwargwadon girman laifin.

Sabon shirin zai fara biyan kuɗi ga wadanda suka cancanta daga 28 ga Agusta, 2026, yayin da waɗanda suka fito daga tsohon tsarin suka shiga sabon shirin daga 8 ga Satumba za su fara samun biyan kuɗinsu na farko a 25 ga Satumba.

Kamfanin ya ce manufar sabon tsarin ita ce ƙarfafa masu ƙirƙirar abubuwan asali, musamman waɗanda ke kawo sabbin bayanai, ilimi, rahotanni, nishaɗi da ra'ayoyi masu ma'ana a dandalin.

DA DUMI-DUMI

Karyar N23,000 Ta Janyo Tirka-Tirka Tsakanin Ma’aurata – Ku taya mu warware wannan lamari

“Ga account number, turo min da kuɗin da mijina ya ba ki. Na yi ƙarya da sunanki ne, kuma na manta ban gaya miki ba.”

Inverter AC da Non-Inverter AC : Menene bambancinsu kuma wanne ya fi?

Abu mafi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa an zaɓi AC mai daidai da girman ɗakin. Ko Inverter ce ko Non-Inverter, AC mai girma fiye da abin da ɗakin ke buƙata ba lallai ta kasance mafi inganci ba.

Me Ya Sa Wayoyin Zamani Suka Daina Yin Batirin Da Ake Iya Cirewa, Kuma Me Ya Sa Ake Son Dawo Da Shi?

Amma a yau, mafi yawan wayoyin zamani suna zuwa da batir da aka kulle a cikin jikin waya. Sai dai wannan yanayin na iya fara sauyawa daga shekara mai zuwa, musamman saboda wata sabuwar dokar Tarayyar Turai.

Jihar Bauchi ta ayyana ɓarkewar cutar kwalara bayan mutuwar mutane 16

Gwamnatin Bauchi ta ce ta ƙaddamar da matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙara sa ido kan masu fama da cutar, inganta cibiyoyin jinya da kuma samar da kayayyakin magani.

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

Kanun Labarai

Mun yi kewar Shehu: Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya

Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"

NLC da TUC sun buƙaci a mayar da mafi ƙarancin albashi daga 70,000 zuwa N500,000

Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.

Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaɓe

Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga 'yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img