CBN: Masu albashin N150,000 zuwa N250,000 sun fi jin radadin tsadar rayuwa a Yuli
Daga Wakiliya
Binciken da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar ya nuna cewa ’yan Najeriya masu samun albashin N150,000 zuwa N250,000 a wata su ne suka fi bayyana cewa tsadar kayayyaki da ayyuka ta yi yawa a watan Yuli.
Rahoton Binciken Tsammanin Hauhawar Farashi na Yuli 2026 da CBN ya fitar ya nuna cewa kashi 71 cikin 100 na mutanen da ke cikin wannan rukunin albashi sun ce hauhawar farashin kayayyaki ta yi yawa.
CBN ya ce kashi 66.2 cikin 100 na masu samun kasa da N70,000 sun bayyana irin wannan ra'ayi, yayin da kashi 66.9 cikin 100 na masu samun N70,000 zuwa N150,000 suka ce haka.
Masu samun N350,001 zuwa N450,000 kuwa su ne suka fi karancin wannan fahimta, inda kashi 55 cikin 100 suka ce farashin kayayyaki ya yi yawa.
A cewar CBN, adadin gidaje da suka ce hauhawar farashi ta yi yawa ya ragu daga kashi 76 a watan Yuni zuwa kashi 67.3 a Yuli.
Bankin ya ce abubuwan da suka fi shafar yadda ’yan Najeriya ke kallon hauhawar farashi sun hada da tsadar makamashi da sufuri, rashin tsaro, matsalolin ababen more rayuwa, canjin kudin musayar waje da kuma ayyukan ’yan tsaka-tsaki.
CBN ya kuma ce gidaje da ’yan kasuwa na sa ran matsin tattalin arziki da kuma kudaden da ake kashewa sakamakon hauhawar farashi za su ragu a cikin watanni shida masu zuwa.





