Karyar N23,000 Ta Janyo Tirka-Tirka Tsakanin Ma’aurata – Ku taya mu warware wannan lamari

Karyar N23,000 Ta Janyo Tirka-Tirka Tsakanin Ma'aurata – Ku taya mu warware wannan lamari

Daga Wakiliya

Salisu Umar Salinga ya wallafa wata tambaya da ta jawo ce-ce-ku-ce kan yadda wasu mata ke ɓoye wa mazajensu wasu abubuwa, musamman batun kuɗi.

Ya ce, misali, mace za ta iya yin wata hidimar gida da kuɗinta, amma idan mijinta ya tambaya sai ta ce ta karɓi bashin kuɗin ne a wurin wata kawar ta, da nufin idan ya samu kuɗi ya biya.

Ya kawo wani labari da ya ce yanzu haka ya jawo tirka-tirka tsakanin wata mata da kawar ga.

A cewar Salisu Umar Salinga, wata mata ta yi ƙarya da sunan wata mace, inda ta gaya wa mijinta cewa ta karɓi bashin N23,000 daga wurin wannan matar.

Da mijin ya samu kuɗin, sai ya kai wa matar da aka ambata kuɗin, har ma ya ƙara mata N10,000 a matsayin kyautatawa.

Sai bayan ya koma gida ne ya gaya wa matarsa cewa ya biya matar da ta ba ta bashin N23,000, sannan ya ƙara mata N10,000.

A nan ne matar ta shiga wani hali, domin ba za ta iya gaya wa mijinta cewa ashe ƙarya ta yi ba.

Daga baya, bayan mijin ya koma wurin aiki, sai matar ta kira waccan mace, ta nemi ta turo mata da kuɗin zuwa asusunta:

“Ga account number, turo min da kuɗin da mijina ya ba ki. Na yi ƙarya da sunanki ne, kuma na manta ban gaya miki ba.”

Sai matar ta amsa mata cewa ita ba ta san komai game da wannan magana ba, kuma ba za ta maida mata da kudin ba.

Yanzu dai abin ya rikice, ana ƙoƙarin gano yadda za a warware wannan matsala ba tare da ƙarin rikici ko rashin fahimta ba.

A ganinku, shin ya dace mutum ya yi amfani da sunan wani wajen ɓoye wa mijinsa ko matarsa gaskiyar abin da ya faru musamman akan kuɗi?

DA DUMI-DUMI

X (Twitter) ta soke tsarin biya na Revenue Sharing, ta ƙaddamar da sabon tsarin biyan na Original Content Rewards

Kamfanin ya ce manufar sabon tsarin ita ce ƙarfafa masu ƙirƙirar abubuwan asali, musamman waɗanda ke kawo sabbin bayanai, ilimi, rahotanni, nishaɗi da ra'ayoyi masu ma'ana a dandalin.

Inverter AC da Non-Inverter AC : Menene bambancinsu kuma wanne ya fi?

Abu mafi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa an zaɓi AC mai daidai da girman ɗakin. Ko Inverter ce ko Non-Inverter, AC mai girma fiye da abin da ɗakin ke buƙata ba lallai ta kasance mafi inganci ba.

Me Ya Sa Wayoyin Zamani Suka Daina Yin Batirin Da Ake Iya Cirewa, Kuma Me Ya Sa Ake Son Dawo Da Shi?

Amma a yau, mafi yawan wayoyin zamani suna zuwa da batir da aka kulle a cikin jikin waya. Sai dai wannan yanayin na iya fara sauyawa daga shekara mai zuwa, musamman saboda wata sabuwar dokar Tarayyar Turai.

Jihar Bauchi ta ayyana ɓarkewar cutar kwalara bayan mutuwar mutane 16

Gwamnatin Bauchi ta ce ta ƙaddamar da matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙara sa ido kan masu fama da cutar, inganta cibiyoyin jinya da kuma samar da kayayyakin magani.

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

Kanun Labarai

Mun yi kewar Shehu: Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya

Tinubu ya yaba wa Ɗariƙar Tijjaniyya kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen yaɗa addinin Musulunci a duniya ya ce "har yanzu muna kewar Uban mu kuma jagora Nagari Sheikh Dahiru Bauchi"

NLC da TUC sun buƙaci a mayar da mafi ƙarancin albashi daga 70,000 zuwa N500,000

Ya ce, la'akari da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ma'aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da bukatunsu ba.

Yan Conservative sun yi alkawarin hana ‘yan Najeriya samun gidajen gwamnati a Birtaniya idan suka lashe zaɓe

Jam'iyyar ta ce matakin zai iya samar da gidaje sama da 228,000 ga 'yan Birtaniya, yayin da kasar ke fama da karancin gidaje da kuma dogayen jerin masu jiran samun matsuguni.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img