Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure – inji Ma’aurata a Auren Gatan da Akayi a Kano
Daga Wakiliya
Wasu ma’aurata da suka amfana da shirin auren gata na gwamnatin Kano sun bayyana farin cikinsu bayan da suka samu damar aure, duk da cewa tsadar rayuwa ta hana su yin hakan tsawon shekaru.
A ranar Juma’a ne gwamnatin Kano ta daura wa kusan ’yan mata da zawarawa 1,500 da kuma mazaje 1,500 aure a wani bikin auren gata da ake gudanarwa duk shekara a jihar.
An zaɓi ma’auratan ne daga kananan hukumomi 44 na jihar, domin taimaka wa mutanen da ke son yin aure amma ba su da isassun kudaden gudanar da bikin.
An gudanar da bikin ne a fadar Sarkin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wakilci iyayen amaren, yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya wakilci mazajen.
Babban Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya jagoranci daurin auren.
Da yake magana da majiyar Wakiliya, ango Aliyu Ibrahim Beli, wanda ya auri Amina Aminu Beli, ya ce sun shafe shekaru fiye da uku suna soyayya amma rashin hali ya hana su aure.
“Mun shafe shekara uku muna soyayya, ni da Amina, amma tsadar rayuwa ta hana mu cika burinmu na aure har zuwa yau, lokacin da muka samu damar yin aure ta hanyar wannan shirin da gwamnati ta shirya,” in ji shi.
Amina Aminu Beli ta ce babu abin da za ta iya cewa a ranar aurensu illa godiya ga Allah.
Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.




