Kungiyar Ƙasashen Musulmi (MWL) za ta ƙaddamar da cibiyar kula da zuciya a Kaduna
Daga Wakiliya
Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya, Muslim World League za ta ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar kula da cututtukan zuciya a Tudun Wada, cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.
Za a gudanar da bikin ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, inda Sakataren-Janar na Muslim World League, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, zai jagoranci bikin.
Daraktan-Janar na hukumar addini ta Kaduna State Interfaith Bureau, Malam Tahir Umar Tahir, ya ce cibiyar za ta samar da ingantaccen gwaji, magani da kulawa ga masu fama da cututtukan zuciya.
Ya ce cibiyar hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin Kaduna da Muslim World League, kuma za ta duba marasa lafiya ba tare da la’akari da addininsu ba.
A cewar Tahir, cibiyar za ta taimaka wajen rage yawan mutanen da ke fita ƙasar waje domin neman maganin cututtukan zuciya.
Sabuwar cibiyar kula da zuciyar za ta ƙara yawan kwararrun cibiyoyin kiwon lafiya a Kaduna, bayan Bola Ahmed Tinubu Specialist Hospital da aka ƙaddamar a jihar a watan Yunin 2025.





