Rashin Wuta Bayan 7 Na Yamma Na Sa ’Yan Najeriya Ƙara Haihuwa, Saboda suna komawa gida da wuri su kasance tare da matansu — Fayose
Daga Wakiliya
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya danganta rashin wutar lantarki a yankunan karkara da yin barci da wuri, da kuma abin da ya ce na iya haifar da ƙarin yawan haihuwa.
Ayodele Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki a Karkara (REA).
A wani faifan bidiyo da ARISE News ta wallafa a ranar Asabar, Fayose ya ce rashin wutar lantarki na barin mazauna yankunan karkara ba tare da wasu hanyoyin nishaɗi ba da daddare.
Ya ce idan dare ya yi, musamman bayan ƙarfe 7 na yamma, mutane kan koma gidajensu, inda hakan ke sa su kasance tare da matansu, lamarin da ya ce na iya ƙara yawan jama'a.
Fayose ya ce samar da wutar lantarki a yankunan karkara zai ba mutane damar samun wasu hanyoyin nishaɗi, ciki har da harkokin dare, maimakon komawa gida da wuri.
An rantsar da Ayodele Fayose tare da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na REA daga hannun Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe.
Hukumar REA ce ke da alhakin taimakawa wajen faɗaɗa samar da wutar lantarki ga al'ummomin da ba su da wuta ko kuma ke samun ƙarancin wutar lantarki a Najeriya.
An kuma rantsar da Ahmadu Abubakar da Ilyasu Makinta a matsayin mambobin kwamitin, yayin da Abba Aliyu ya karɓi ragamar shugabancin hukumar a matsayin Darakta-Janar.




