Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.
Sai dai APC ta ce tana ci gaba da duba sakamakon da yadda aka gudanar da zaɓen, wanda zai iya zama matakin farko na ƙalubalantar sakamakon da aka sanar.
Wike ya umarci rushe gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa a Abuja
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja.
Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata.
Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba.
Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin 'yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa.
Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja.
Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,
Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar.
Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.
Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.
Ta haihu babu ko tsinke na haiuwa daga mijin, ya ki rako ta Asibiti, babu wani nashi kuma ko sisi bai bayar ba, ita ce matar shi ta huɗu, haihuwa na 11, yan uwanta suke komai, tana cikin nakuda ma sai da tayi mashi tuwo kafin ta taho Asibiti....
Ya kuma ce abin da ya faru da shi ya kara tabbatar masa da bukatar gwamnati ta magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da karancin ilimi, wadanda ya ce suna taimakawa wajen yaduwar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.