Rahotanni

Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

Yanzu dai ana sa ran sabon jerin kwamitin zai ƙara wakiltar sassa daban-daban na jam’iyyar tare da shigar da manyan jiga-jiganta kafin fara babban yaƙin neman zaɓen 2027.

Farashin kayayyaki na raguwa a takarda, amma a zahiri farashin abinci na ƙaruwa, talakawa na fama da matsin rayuwa – Masana

Daga cikin matakan da ya ba da shawara akwai sakin hatsin da ke cikin rumbunan ajiyar gwamnati zuwa wuraren da ake fama da tsananin ƙarancin abinci, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan ambaliyar ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.

Gwamnatin Birtaniya ta bukaci Musulmi su rage amfani da ruwa wajen alwala

Wasu masu fafutukar kare hakkin al'umma sun kuma ce Musulunci kansa ya yi kira da a guji barnatar da ruwa yayin alwala (almubazzaranci haramun ne a musulunci).

Rayuwar Alkali Bunza a Hannun Masu Garkuwa: Ya Ce Ya Yi Tafiyar Kilomita 25 Ba Takalmi

Ya kuma ce abin da ya faru da shi ya kara tabbatar masa da bukatar gwamnati ta magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da karancin ilimi, wadanda ya ce suna taimakawa wajen yaduwar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.

Akalla makarantun firamare da sakandare 65 sun daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro -rahoto

makarantun suna jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatun yara a wasu sassan Katsina da Adamawa.

Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure  – inji ma’auratan da aka yi wa Auren Gata...

Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi

Kungiyar Ƙasashen Musulmi (MWL) za ta ƙaddamar da cibiyar kula da zuciya a Kaduna

Ya ce cibiyar hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin Kaduna da Muslim World League, kuma za ta duba marasa lafiya ba tare da la’akari da addininsu ba.

Mutumin Kano da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida bara ya sake aure

Mutumin Kano da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida bara ya sake aure - yana cikin wadanda aka yiwa auren gata  Daga Wakiliya Wani mutum a Kano, Malam Haruna Bashir, wanda aka kashe wa mata da ’ya’yansa shida a shekarar da ta gabata, ya sake aure, yana cikin wadanda aka yi wa auren gata da gwamnatin jihar ta shirya. An kashe matar Malam Haruna da ’ya’yansa shida ne a harin da wasu matasa dauke da makamai suka kai gidansu da ke yankin Dorayi a Kano. Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Kano ta yi alkawarin samar masa da sabon gida tare da daukar nauyin sake aurensa. A ranar Juma’a ne aka cika alkawarin, inda aka daura wa Malam Haruna aure a bikin Auren Gata da aka gudanar a fadar Sarkin Kano. An saka sunansa cikin maza 1,500 da suka yi aure a bikin da hukumar Hisbah ta jihar ta shirya. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya jagoranci daurin auren, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya a matsayin waliyyin amaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kuma ya wakilci angwaye.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img