SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

Daga Wakiliya

Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantu a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da ke jihar saboda matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala, ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin tarayya.

Ya ce dukkan makarantun jihar, ciki har da na firamare, za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyin yanayin tsaro.

Sai dai an ware kananan hukumomin Sokoto North, Sokoto South da Wamakko daga matakin rufewar.

Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.

Ya ce a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Aminu Tambuwal, an mayar da wasu makarantun kwana zuwa cikin birnin Sokoto saboda matsalar tsaro.

Wakiliya ta ruwaito, binciken Sunday Vanguard ya gano makarantu 14 da lamarin ya shafa kai tsaye, ciki har da makarantun sakandare da na fasaha a Tureta, Tangaza, Bodinga, Tambuwal, Goronyo, Gudu, Gwadabawa, Illela, Yabo, Rabah, Binji, Kebbe, Dange da Shagari.

Manir Muhammad Dan’iya, dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a jihar, ya ce rufe makarantun babban koma baya ne ga ilimi da bunkasar al'umma.

Ya ce dubban yara ne suka rasa damar zuwa makaranta sakamakon matakin.

DA DUMI-DUMI

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu -Aregbesola

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Shan ruwan ’ya’yan itace (smoothie) a kullum na iya rage cutar damuwa (depression) – bincike

Saboda haka, suna ganin akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko shan ruwan ’ya’yan itace a kai a kai na da tasiri kai tsaye wajen rage alamun damuwa. Binciken an wallafa shi a mujallar British Journal of Nutrition, kuma Fruit Juice Science Centre ce ta ɗauki nauyin gudanar da shi.

Da kafa Tinubu ke zuwa ofis, kuma sau É—aya yake cin abinci a rana – Shugaban NRS, Zacch Adedeji

Kan yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da hukumomi da ma’aikatu, shugaban NRS ya ce bai kamata a rika kallon kuɗin da gwamnati ke kashewa kawai ba, domin akwai kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da kuma kuɗaɗen da take samarwa ta hanyar waɗannan ayyukan.

Nazari: Yadda rashin tsaro ke kara jefa yaran Arewa cikin matsalar rashin zuwa makaranta

Ya kuma yi gargadin cewa yaran da ba sa makaranta na iya zama masu saukin fadawa hannun kungiyoyin 'yan ta'adda, 'yan bindiga da sauran kungiyoyin aikata laifuka.

Kanun Labarai

Babu gaskiya a labarin cewa Sarki Sanusi ya samu ‘carry over’ — Masarautar Kano

Masarautar ta kuma ce bidiyon da ake yaɗawa an dauke shi ne yayin wani shiri da ɗaliban Shari’a suka gudanar, inda wasu matasa suka shirya shi da nufin yaɗa bayanan ƙarya.

Tinubu ya nemi haɗin kan Tijjaniyya wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Najeriya da yankin Sahel

Tinubu ya ce ya kamata malaman addini su riƙa jan hankalin shugabannin siyasa kan adalci, ɗaukar nauyi da tausayi, tare da jan hankalin jama’a da kada su mayar da ƙorafe-ƙorafe zuwa hujjar aikata rashin doka.

Kalaman Jingir na da matuƙar tayar da hankali— Fani-Kayode ya caccaki malamin kan salon tallata tikitin Musulmi-Musulmi

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Musulmi su mallaki katunan zaɓensu domin tunkarar zaɓen.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img