Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

DG Abdul’Aziz Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin sake duba tare da gyara jerin sunayen kwamitin yakin neman zaɓen jam’iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Rahotanni sun ce matakin ya biyo bayan koke-koken wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka nuna cewa jerin farko bai yi la’akari da wasu muhimman shugabanni da kuma tsarin rabon mukamai tsakanin yankuna ba.

An ce Shugaba Tinubu ya umarci ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, tare da shugabannin Majalisar Ƙasa da Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na APC, da su sake tsara jerin sunayen.

A jerin farko, tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, ne aka nada Darakta-Janar na kwamitin.

Sai dai rashin sanya sunan Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya jawo suka, musamman daga wasu masu ruwa da tsaki a Kudu maso Gabas.

Haka kuma, yadda aka tsara mukaman shugabannin Majalisar Ƙasa ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka sanya Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a matsayin Mataimakin Darakta-Janar na bangaren yakin neman zaɓen Kudu.

Wasu daga cikin jiga-jigan APC sun ce ya kamata a bai wa Akpabio matsayi da ya dace da matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa, bisa tsarin shugabanci na ƙasa.

Rahotanni sun kuma ce jerin farko bai ƙunshi wasu daga cikin fitattun ‘yan jam’iyyar da suka taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaɓen APC na 2023 ba.

Daga cikinsu akwai tsohon Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaɓen 2023, Simon Lalong; Ministan Jiragen Sama da Sararin Samaniya, Festus Keyamo; mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Haka kuma, tsoffin gwamnoni Gbenga Daniel da Ibikunle Amosun, da tsohon ɗan takarar gwamnan Edo, Osagie Ize-Iyamu, ba su cikin jerin.

Rahotanni sun ce rashin sanya sunan Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, shi ma ya jawo damuwa saboda muhimmancin gwamnoni wajen tattara magoya bayan jam’iyya a jihohinsu.

Sai dai babu wata alama da ke nuna cewa Shugaba Tinubu ya sauya matsayinsa kan nadin Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar.

A yayin da ake sake tsara kwamitin, Shugaba Tinubu ya bukaci waɗanda aka ambata a jerin farko da su fara aikin ƙarfafa jam’iyya da wayar da kan jama’a kan nasarorin gwamnatinsa da sauye-sauyen tattalin arziki.

Ya ce APC na da nasarorin da za ta gabatar wa al’umma yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa.

Yanzu dai ana sa ran sabon jerin kwamitin zai ƙara wakiltar sassa daban-daban na jam’iyyar tare da shigar da manyan jiga-jiganta kafin fara babban yaƙin neman zaɓen 2027.

DA DUMI-DUMI

Maza ba wawaye bane: Ba za ki yi wa mijinki rashin kunya sannan ki sa ran zai ci gaba da sonki ba – Zainab

Jamiu Zainab ta ce wasu mata ba sa son a yi musu gyara, kuma kan yi gardama ko mayar da magana idan mazajensu suka yi magana da su.

Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 –  Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa

Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.

Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari 

Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.

Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai

Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.

Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris

Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.

Kanun Labarai

Wani Magidanci ya nemi Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda tana zuba ruwa kan gadon idan ya nemi saduwa da ita

Alkalin kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce bayan duba lamarin, ya amince da bukatar Dauda tare da rusa auren nasu.

Farashin kayayyaki na raguwa a takarda, amma a zahiri farashin abinci na ƙaruwa, talakawa na fama da matsin rayuwa – Masana

Daga cikin matakan da ya ba da shawara akwai sakin hatsin da ke cikin rumbunan ajiyar gwamnati zuwa wuraren da ake fama da tsananin ƙarancin abinci, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan ambaliyar ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.

1 cikin 4 na mazan da aka yiwa Gwajin DNA a Najeriya ba su ne ubannin yaransu ba – Rahoto

Rahoton ya ce maza masu shekaru 41 zuwa sama ne suka fi yawa cikin wadanda suka nemi gwajin, inda suka kai kashi 48 cikin 100.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img