Akalla makarantun firamare da sakandare 65 sun daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro -rahoto

Akalla Makarantun firamare da Sakandare 65 suka daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda matsalar tsaro

Daga Wakiliya

Akalla makarantu 65 na firamare da sakandare ne suka daina aiki ko kuma aka rufe su saboda rashin tsaro a wasu sassan arewacin Najeriya.

Wakiliya ta ruwaito binciken Vanguard ya gano cewa makarantun suna jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatun yara a wasu sassan Katsina da Adamawa.

Dalilan rufe makarantun sun hada da hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyin ta'addanci, sace dalibai, kauracewar al'ummomi da kuma fargabar sake kai hare-hare kan dalibai da malamai.

A wasu wurare, makarantu sun shafe tsawon lokaci a rufe. A wasu kuma, an mayar da dalibai zuwa makarantu da ake ganin sun fi tsaro ko kuma aka hade makarantu domin ci gaba da karatun yara.

Masana ilimi sun ce ci gaba da rufe makarantu na iya kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, tare da haifar da matsaloli masu dorewa ga makomar yaran.

Wannan na faruwa ne duk da shirye-shiryen da gwamnatin Najeriya da kungiyoyin kasa da kasa suka samar domin kare makarantu daga hare-hare.

DA DUMI-DUMI

Tinubu ya sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya — Shugaban NRS Zacch Adedeji

Ya kawo misalin Andy Burnham na Birtaniya, inda ya ce ya ɗauki matakai da suka haɗa da rage haraji kan wutar lantarki ta gidaje da kuma rage kuɗin sufuri domin sauƙaƙa wa jama’a.

Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure  – inji ma’auratan da aka yi wa Auren Gata...

Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi

Masu Karbar Albashin N150,000 zuwa N250,000 sun fi jin radadin tsadar rayuwa a Yuli -CBN

Bankin ya ce abubuwan da suka fi shafar yadda ’yan Najeriya ke kallon hauhawar farashi sun hada da tsadar makamashi da sufuri, rashin tsaro, matsalolin ababen more rayuwa, canjin kudin musayar waje da kuma ayyukan ’yan tsaka-tsaki.

Rashin Wuta Bayan 7 Na Yamma Na Sa ’Yan Najeriya Ƙara Haihuwa  — Fayose

Rashin Wuta Bayan 7 Na Yamma Na Sa ’Yan Najeriya Ƙara Haihuwa, Saboda suna komawa gida da wuri su kasance tare da matansu  — Fayose

Kanun Labarai

Kungiyar Ƙasashen Musulmi (MWL) za ta ƙaddamar da cibiyar kula da zuciya a Kaduna

Ya ce cibiyar hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin Kaduna da Muslim World League, kuma za ta duba marasa lafiya ba tare da la’akari da addininsu ba.

Mutumin Kano da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida bara ya sake aure

Mutumin Kano da aka kashe wa mata da ’ya’ya shida bara ya sake aure - yana cikin wadanda aka yiwa auren gata  Daga Wakiliya Wani mutum a Kano, Malam Haruna Bashir, wanda aka kashe wa mata da ’ya’yansa shida a shekarar da ta gabata, ya sake aure, yana cikin wadanda aka yi wa auren gata da gwamnatin jihar ta shirya. An kashe matar Malam Haruna da ’ya’yansa shida ne a harin da wasu matasa dauke da makamai suka kai gidansu da ke yankin Dorayi a Kano. Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Kano ta yi alkawarin samar masa da sabon gida tare da daukar nauyin sake aurensa. A ranar Juma’a ne aka cika alkawarin, inda aka daura wa Malam Haruna aure a bikin Auren Gata da aka gudanar a fadar Sarkin Kano. An saka sunansa cikin maza 1,500 da suka yi aure a bikin da hukumar Hisbah ta jihar ta shirya. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya jagoranci daurin auren, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya a matsayin waliyyin amaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kuma ya wakilci angwaye.

Karyar N23,000 Ta Janyo Tirka-Tirka Tsakanin Ma’aurata – Ku taya mu warware wannan lamari

“Ga account number, turo min da kuɗin da mijina ya ba ki. Na yi ƙarya da sunanki ne, kuma na manta ban gaya miki ba.”
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img