Abin da ya ba su damar ci gaba da zama a NNPC ba takardar aiki ba ce, aikinsu ne da suka nuna cikin shekara guda da suka yi suna aiki ƙarƙashin matsin lamba," in ji Ojulari.
Jagorar binciken, Farfesa Margherita Fontana ta Jami'ar Michigan, ta ce maganin yana da matuƙar aminci har ma ga yara masu shekara ɗaya, kuma zai iya taimaka wa yara ƙanana, tsofaffi, masu nakasa da kuma mutanen da ke tsoron zuwa wurin likitan haƙori.
Hakazalika, ya buƙaci masu gadi da jami'an tsaro da ke kula da makarantu da sauran cibiyoyin gwamnati su ƙara sanya ido, sannan ya yi kira ga al'umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ɓarna a jihar.
A shekarar 2016, rundunar sojin Indiya ta tilasta wa sama da mutum 1,150 da ke rubuta jarabawar ɗaukar sojoji a jihar Bihar su cire dukkan tufafinsu, sai dai kayan ciki (underwear) kaɗai.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.