Masana Sun Gano Hanyar Dakatar da Lalacewar Haƙora Ba Tare da Cire Shi ba

Masana Sun Gano Hanyar Dakatar da Lalacewar Haƙora Ba Tare da An Cire Shi Ba

Daga Wakiliya

Masana kimiyya a Amurka sun gano cewa wani magani mai ruwa da ake kira Silver Diamine Fluoride (SDF) na iya dakatar da lalacewar haƙora ba tare da an cire haƙorin ko an yi allurar kashe zafi ba.

Wani babban bincike da aka wallafa a mujallar JAMA Pediatrics ya nuna cewa shafa maganin SDF mai ƙarfi kashi 38 cikin ɗari a kan haƙoran yara masu ƙasa da shekara shida duk bayan watanni shida ya dakatar da ci gaban lalacewar haƙora a fiye da rabin haƙoran da aka yi wa maganin.

Masu binciken sun ce ana shafa maganin ne cikin daƙiƙu kaɗan ta amfani da ƙaramin auduga, ba tare da buƙatar cire haƙorin ko allura ko sa barci ba. Sai dai maganin yana sa wurin da haƙorin ya lalace ya koma baƙi har abada.

Jagorar binciken, Farfesa Margherita Fontana ta Jami’ar Michigan, ta ce maganin yana da matuƙar aminci har ma ga yara masu shekara ɗaya, kuma zai iya taimaka wa yara ƙanana, tsofaffi, masu nakasa da kuma mutanen da ke tsoron zuwa wurin likitan haƙori.

Binciken ya haɗa da yara 830 daga jihohin Michigan, New York da Iowa, kuma masana sun ce sakamakon zai iya taimakawa Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da amfani da SDF a hukumance wajen magance lalacewar haƙora.

Masana sun yi imanin cewa idan aka amince da maganin, zai taimaka wajen rage ciwon haƙora, kamuwa da cututtuka da kuma buƙatar yi wa yara tiyata saboda matsalar lalacewar haƙora.

DA DUMI-DUMI

NNPC Ta Ɗauki Sabbin Ma’aikata Fiye da 1,000 Har Sun Fara Aiki Bayan Basu Horo Na Shekara Guda – Ojulari

Abin da ya ba su damar ci gaba da zama a NNPC ba takardar aiki ba ce, aikinsu ne da suka nuna cikin shekara guda da suka yi suna aiki ƙarƙashin matsin lamba," in ji Ojulari.

Kotu a Rasha Ta Kwace Kadarori 123 Mallakin Ƙungiyar Kiristoci ta Jehovah’s Witnesses

Sai dai a shekarar 2022, Kotun Kare Haƙƙin Bil Adama ta Turai ta yanke hukuncin cewa haramta ƙungiyar ya saɓa wa doka.

KO KUN SAN? Hadiza Miller, Matar da Ta Wakilci Zariya a Majalisar Dokokin Kaduna a 1983

Hajiya Hadiza Miller ita ce 'yar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ta wakilci mazabar Zariya a shekarar 1983, a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Biza Da Fasfo: Amurka Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Amfani da Hotunan Fasfo da AI Ta Gyara

Sanarwar ta ce kada masu neman biza ko fasfo su yi amfani da AI, filtoci (filters), ko wani nau'in gyaran hoto na dijital yayin ɗaukar hoton fasfo.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus Ko Ta Tsige Shi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus, Akwai Shakku A Shugabancinsa

Kanun Labarai

Barayi Sun Kutsa Makarantar Gwamnati a Jigawa Sun Yi Wa Masu Gadi Duka Sun Sace Kayan Wutan Lantarkin Makarantar

Hakazalika, ya buƙaci masu gadi da jami'an tsaro da ke kula da makarantu da sauran cibiyoyin gwamnati su ƙara sanya ido, sannan ya yi kira ga al'umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ɓarna a jihar.

TSOKACI: Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img