NNPC Ta Ɗauki Sabbin Ma’aikata Fiye da 1,000 Har Sun Fara Aiki Bayan Basu Horo Na Shekara Guda – Ojulari
Daga Wakiliya
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Ltd) ya sanar da tura sabbin ma’aikata sama da 1,000 aiki bayan sun shafe shekara guda suna aikin horaswa (internship), samun horo na musamman da kuma tantance ƙwarewarsu.
Babban Jami’in Gudanarwa na NNPC Ltd, Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa matakin wani babban ci gaba ne ga kamfanin.
A cewarsa, sabbin ma’aikatan sun samu gurbin ne bayan sun tsallake tsauraran matakan horaswa da tantance aiki, ba tare da la’akari da alaƙa ko yankin da suka fito ba.
“Abin da ya ba su damar ci gaba da zama a NNPC ba takardar aiki ba ce, aikinsu ne da suka nuna cikin shekara guda da suka yi suna aiki ƙarƙashin matsin lamba,” in ji Ojulari.
Ya ce tsarin ɗaukar ma’aikatan NNPC yanzu ya dogara ne da ƙwarewa, jajircewa da adalci, ba sanin wani ko asalin mutum ba.
Ojulari ya kuma ƙarfafi sabbin ma’aikatan da su kasance masu kawo sabbin dabaru, bayyana ra’ayoyinsu da kuma ɗaukar alhakin ci gaban sana’arsu.
Ya kuma tunatar da su kada su manta da irin tafiyar da suka bi kafin samun wannan dama, tare da kira gare su da su ma su ba wasu damar irin wannan idan suka samu iko a gaba.
An fara wannan shirin ɗaukar ma’aikatan ne a watan Yulin 2024 a lokacin tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na NNPC, Mele Kyari, kuma ya zo daidai da ƙoƙarin kamfanin na ƙarfafa ma’aikatansa bayan sauyawa zuwa kamfani mai gudanar da harkokinsa bisa tsarin kasuwanci ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).





