Barayi Sun Kutsa Makarantar Gwamnati a Jigawa Sun Yi Wa Masu Gadi Duka Sun Sace Kayan Wutan Lantarkin Makarantar

Barayi Sun Kutsa Makarantar Gwamnati a Jigawa Sun Yi Wa Masu Gadi Duka Sun Sace Kayan Wutan Lantarkin Makarantar

Daga Wakiliya

Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun kutsa cikin Makarantar Government Unity School da ke Ringim a Jihar Jigawa, inda suka yi wa masu gadin makarantar duka tare da sace mita 12 na kebul mai sulke (armoured cable) da ke haɗe da tiransifomar makarantar.

Mai magana da yawun Hukumar NSCDC ta Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026, lokacin da sama da mutum 10 suka mamaye makarantar, suka yi galaba kan masu gadin guda uku kafin su yanke kebul ɗin suka tsere.

Ya bayyana cewa darajar kebul ɗin da aka sace na tsakanin Naira 900,000 zuwa miliyan 1.05, lamarin da ya jefa makarantar cikin duhu.

Tijjani ya ce jami’an NSCDC na shiyyar Ringim sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa, inda suka tattara wasu shaidu da za su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata laifin.

A nasa martanin, Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, CC Muhammad Ingawa, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin hari kan muhimman kadarorin gwamnati.

Ya umarci jami’ansa su ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargi, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Hakazalika, ya buƙaci masu gadi da jami’an tsaro da ke kula da makarantu da sauran cibiyoyin gwamnati su ƙara sanya ido, sannan ya yi kira ga al’umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ɓarna a jihar.

DA DUMI-DUMI

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus Ko Ta Tsige Shi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus, Akwai Shakku A Shugabancinsa

TSOKACI: Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Rundunar sojin Indiya ta taba tilasta wa masu neman Soja rubuta jarabawa daga su sai dan kamfe don gudun satar jarabawa

A shekarar 2016, rundunar sojin Indiya ta tilasta wa sama da mutum 1,150 da ke rubuta jarabawar ɗaukar sojoji a jihar Bihar su cire dukkan tufafinsu, sai dai kayan ciki (underwear) kaɗai.

Remi Tinubu Ta Shawarci Matasan Najeriya Su Koyi Wadatar Zuci, Su Guji Kwaɗayi da Maular Abin Hannun Wasu

"Ku koyi gamsuwa da abin da kuke da shi, kada ku zama masu kwaɗayi ko roƙon abin hannun wasu," in ji ta.

Kanun Labarai

TSOKACI: Tattalin Arziki na Inganta ga Tinubu, Amma Yana Ƙara Tsananta wa Talakawa

Tattalin Arziki na Inganta ga Tinubu, Amma na Ƙara Tsananta wa Talakawa — Adekunle Adekoya

Lauya Ya Yi Barazanar Kai NYSC Kara Kan Sharadin Tilasta wa Matan Aure Sauya Sunan Iyayensu

Lauya Ya Yi Barazanar Kai NYSC Kotu Kan Sharadin Tilasta wa Matan Aure Sauya Sunan Iyayensu

Gwamnatin Abia Ta Sanya Harajin Naira miliyan 200 da Miliyan 150 Ga Duk Dan takarar Shugaban Ƙasa da Gwamna Dake Son Saka Allon...

Gwamnatin Abia Ta Sanya Kuɗin Lasisin Allon Yaƙin Neman Zaɓe: Naira Miliyan 200 ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Miliyan 150 ga Na Gwamna Daga Wakiliya Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa duk ɗan takarar shugaban ƙasa da ke son kafa allunan yaƙin neman zaɓe (billboards) da fastoci a jihar zai biya Naira miliyan 200 domin samun lasisin yin hakan. Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamomin Kasuwanci ta Jihar Abia (ABSSAA) ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Aba. Shugaban Sashen Dabaru, Ƙirkire-ƙirkire da Tsara na hukumar, Ndubuisi Nwaogwugwu, ya ce jadawalin kuɗaɗen ya shafi dukkan 'yan takara a matakai daban-daban. A cewarsa, ɗan takarar gwamna zai biya Naira miliyan 150, ɗan takarar Sanata Naira miliyan 100, ɗan takarar Majalisar Wakilai Naira miliyan 50, yayin da ɗan takarar Majalisar Dokokin Jiha zai biya Naira miliyan 20. Darakta Janar na Ofishin Sadarwa na Gwamnatin Abia, Onyebuchi Ememanka, ya ce tsarin ba abin cece-kuce ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce tabbatar da tsaro, tsaftar muhalli da kuma gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsari. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta nuna bambanci ga kowace jam'iyya ko ɗan takara ba, muddin an bi ƙa'idoji kuma an biya kuɗin da aka tanada. Sai dai Ƙungiyar Masu Tallace-tallace ta Waje ta Najeriya (OAAN) ta nuna damuwa kan sabon jadawalin kuɗin, tana mai cewa kuɗaɗen sun yi tsauri kuma za su iya kawo cikas ga tallan siyasa a jihar. Shi ma shugaban jam'iyyar ADC a Abia, Kalu Kalu, ya ce idan dokar jihar ta tanadi irin waɗannan kuɗaɗe jam'iyyarsa za ta biya. Amma idan ba haka ba ne, ya kamata a soke tsarin. Ya kuma yi nuni da cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya bai wa ƙananan hukumomi ikon karɓar irin waɗannan kuɗaɗe, yana mai gargadin cewa duk wata doka da ta saɓa wa Dokar Zaɓe ba za ta dore ba.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img