KO KUN SAN:
A shekarar 2016, rundunar sojin Indiya ta tilasta wa sama da mutum 1,150 da ke rubuta jarabawar ɗaukar sojoji a jihar Bihar su cire dukkan tufafinsu, sai dai kayan ciki (underwear) kaɗai.
An zaunar da su a fili suna rubuta jarabawar, yayin da sojoji ke sa ido a kansu domin hana maguɗin jarabawa, kamar ɓoye takardu ko wayoyin hannu.
An ɗauki wannan mataki ne saboda matsalar satar amsa da maguɗin jarabawa da ta daɗe tana addabar yankin, tare da sauƙaƙa binciken dubban masu rubuta jarabawar.
Sai dai lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar. Ma’aikatar Tsaron Indiya ta nemi bayani daga rundunar soji, kotu kuma ta shiga cikin batun. Daga baya rundunar sojin ta nuna nadama tare da alƙawarin ɗaukar matakan da za su hana irin hakan sake faruwa.





