DAMBARWAR WAK’AR RARARA: BUKATAR TSABTACE TSARIN SIYASAR MU
A GANI NA…..
Banga dalilin da waka’r da mawak’i Dauda Kahutu Rarara da ke tada k’ura; wadda ake zargin yayi ma Prof. isa Ali Pantami, zata tada irin wannan k’urar ba bisa ga dalilin cewa ba sabon abu bane Rarara yayi. Hasali ma, abu ne yayi wanda kowa yasan ya saba yi kuma babu wata shaida mai nuna cewa al’umma basu gamsu da hakan ba.
MU AUNA, MU YI MA RARARA ADALCI….
Wak’a da shaharar Rarara sun ginu ne bisa wak’ar zambo ta siyasa. A baya, yayi manyan mutane, masu mutunci da dimbin mabaya wak’ok’i na zambo. Cikin wak’ok’in shi da suka fi shahara Akwai “Malam Yaci Kudin Makamai” wadda a ciki yayi shaguben da ake zargin tsohon Gwamna Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau yake.
Rarara yayi wak’ar “Tsula ya shiga tsilla tsilla” wadda da yawan mutane sun fahimci cewa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabi’u Kwankwaso yake. Akwai kuma wak’okin shi “Zuwan mai malfa Kano” da “Mai malfa ya karaya” ciki inda ya rika jero manyan jiga-jigan jam’iyar PDP na lokacin cikin shagube yana yi masu zambo.
Wak’ar kuma da nike tunanin ita ta fiddo Rarara sosai a fagen mawak’an siyasa itace wak’ar “Masu gudu su gudu.” A cikin wak’ar babu wani wanda ya amsa sunan shi a jiga-jigan gwamnati da PDP da kuma makusan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan wanda ba ayi ma zambo na shagube ba kama daga shi kanshi Jonathan, mataimakin shi, matar shi har zuwa kan shugabanni jam’iyar PDP na jihohi na lokacin. A cikin har shaguben da ake zargin da mataimakan shugaban kasa na lokacin, Arc. Namadi Sambo yake inda yayi zargin cewa ko Fatiha Namadi Sambo bai iya ba.
A lokacin wak’ar “Masu gudu Su gudu” ta samu karb’uwa sosai ga mafi yawancin yan Arewa; musamman yan jam’iyar APC masu kokarin hamb’are gwamnatin PDP da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ke jagoranta. Har zuwa yanzu ban iya tuna mutum daya wanda muryar shi za tayi tasiri cikin — musamman daga jam’iyar APC ko cikin magoya bayan Marigayi tsohon Shugaban Kasa Buhari, wanda ya fito ya tsawata ma Rarara ko kuma sauran al’ummar da suka maida wak’ar “Masu gudu su gudu” taken budewa da rufe taron Buhari ko na APC ba. Ma’ana, duk mun gamsu cewa zambo da shagube da Rarara ke yi ma shugabanni adawa ba kuskure bane. Mu gamsu cewa idan dai yi ma abokan adawa zambo da shagube zai iya kawo faduwar su zabe, hakan daidai ne a tsarin siyasar mu.
TO MU YI MA KAN MU ADALCI….
Idan dai baka ga kuskure a baya ba lokacin da Rarara ke zambace wadanda ba ra’ayin siyasar ku daya ba, to kau bai kamata ran ka ya baci ko kaga kuskure idan yau ra’ayin siyasar ka yasha banban da na Rarara, ya karkato gangar shi kan gwanin ka ba. A tsarin siyasar mu babu inda Rarara yayi laifi. Shi dai mawaki ne wanda ya ginu kan wakar siyasa. Mu kuma siyasar mu ta ginu kan yarfe, k’azafi da zambo. Wakokin siyasar mu sun ginu kan b’atanci ne maimakon ginuwa kan wanda ake yabo a wak’ar me zai iya yi ya kawo ci gaban al’umma.
Kenan, yadda muka dama kunun mu haka zamu hakura mu sha. Idan dai a baya bamu ga dalilin k’yamar wannan tsarin ba; masu karfin tsawatawa basu tsawata ma Rarara ba tare da yin tir da cin mutuncin abokan adawa ba, to yau fa bamu da hurumin kafa ma Rarara sababbin sharudda na yin wakokin adawa masu tsabta. Hakika mun baro shi tun rani.
A baya dalilai na son chanza gwamnatin Jonathan sun sa mun rufe idanun mu, muka ki ganin rashin daidai cikin tsarin siyasar cin mutunci da wulakanci; hasali ma, sai muka rungumi tsarin, muka rene shi har ya girma. Yau gashi ya juyo kan wasu daga cikin mu (a hankali kuma zai kawo kan kowa). Kenan, yau sai dai muyi hakuri mu ci gaba da girbar abinda muka shuka har mu samu karfin zuciyar da zamu Kalli matsalar a matsayin tsumagiyar kan hanya wadda bata da ido, bugun kowa take yi.
Duk da haka akwai riba cikin dambarwar. Yanzu sai mu zauna mu nazarci dambarwar don fahimtar inda kuskuren yake don mu tsabtace tsarin siyasar mu ta hanyar k’yamatar duk wata da’bi’ar da zata taba mutuncin wani ba tare da kallon wace jam’iya yake ko kuma wanene gwanin shi ba.
Allah Yasa mu dace.
Daga Maiwada Dammallam





