Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus Ko Ta Tsige Shi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus

Daga Wakiliya

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) ta bayyana cewa ta rasa amincewa da shugaban FIFA, Gianni Infantino, tare da buƙatar ya yi murabus daga muƙaminsa bayan rikicin yunƙurin sayar da wani kaso na haƙƙin kasuwancin gasar cin Kofin Duniya.

Rahotanni sun ce Gianni Infantino ya yi ƙoƙarin sayar da kaso mai darajar fam biliyan 3.1 na kasuwancin gasar ga wasu masu zuba jari masu zaman kansu da Josh Kushner ke jagoranta. Sai dai shirin ya rushe bayan ya fuskanci suka masu yawa, lamarin da ya sa shugaban FIFA ya janye daga matakin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, UEFA ta zargi shugabancin FIFA da gudanar da shirye-shirye cikin sirri ba tare da cikakken bayani ko tuntuba ba, tana mai cewa hakan ya janyo rashin amincewa daga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama.

UEFA ta ce za ta yi aiki tare da ƙungiyoyin mambobinta da sauran ƙungiyoyin nahiyoyi domin binciken yadda lamarin ya faru da kuma samar da matakan da za su hana maimaituwarsa. Ta kuma jaddada cewa babu wani zaɓi da ya kamata a cire daga tebur wajen ɗaukar matakin gyara.

Rahotanni sun nuna cewa Æ™asashe mambobin FIFA na iya fara shirin Æ™uri’ar rashin amincewa da Gianni Infantino domin cire shi daga shugabancin Æ™ungiyar. Ana buÆ™atar aÆ™alla Æ™ungiyoyin Æ™wallon Æ™afa 46 daga cikin mambobin FIFA su goyi bayan wannan mataki, yayin da UEFA ita kaÉ—ai ke da mambobi 55.

— Wakiliya

DA DUMI-DUMI

Barayi Sun Kutsa Makarantar Gwamnati a Jigawa Sun Yi Wa Masu Gadi Duka Sun Sace Kayan Wutan Lantarkin Makarantar

Hakazalika, ya buƙaci masu gadi da jami'an tsaro da ke kula da makarantu da sauran cibiyoyin gwamnati su ƙara sanya ido, sannan ya yi kira ga al'umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ɓarna a jihar.

TSOKACI: Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Rundunar sojin Indiya ta taba tilasta wa masu neman Soja rubuta jarabawa daga su sai dan kamfe don gudun satar jarabawa

A shekarar 2016, rundunar sojin Indiya ta tilasta wa sama da mutum 1,150 da ke rubuta jarabawar É—aukar sojoji a jihar Bihar su cire dukkan tufafinsu, sai dai kayan ciki (underwear) kaÉ—ai.

Remi Tinubu Ta Shawarci Matasan Najeriya Su Koyi Wadatar Zuci, Su Guji KwaÉ—ayi da Maular Abin Hannun Wasu

"Ku koyi gamsuwa da abin da kuke da shi, kada ku zama masu kwaɗayi ko roƙon abin hannun wasu," in ji ta.

Kanun Labarai

TSOKACI: Tattalin Arziki na Inganta ga Tinubu, Amma Yana Ƙara Tsananta wa Talakawa

Tattalin Arziki na Inganta ga Tinubu, Amma na Ƙara Tsananta wa Talakawa — Adekunle Adekoya

Lauya Ya Yi Barazanar Kai NYSC Kara Kan Sharadin Tilasta wa Matan Aure Sauya Sunan Iyayensu

Lauya Ya Yi Barazanar Kai NYSC Kotu Kan Sharadin Tilasta wa Matan Aure Sauya Sunan Iyayensu

Gwamnatin Abia Ta Sanya Harajin Naira miliyan 200 da Miliyan 150 Ga Duk Dan takarar Shugaban Ƙasa da Gwamna Dake Son Saka Allon...

Gwamnatin Abia Ta Sanya Kuɗin Lasisin Allon Yaƙin Neman Zaɓe: Naira Miliyan 200 ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Miliyan 150 ga Na Gwamna Daga Wakiliya Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa duk ɗan takarar shugaban ƙasa da ke son kafa allunan yaƙin neman zaɓe (billboards) da fastoci a jihar zai biya Naira miliyan 200 domin samun lasisin yin hakan. Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamomin Kasuwanci ta Jihar Abia (ABSSAA) ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Aba. Shugaban Sashen Dabaru, Ƙirkire-ƙirkire da Tsara na hukumar, Ndubuisi Nwaogwugwu, ya ce jadawalin kuɗaɗen ya shafi dukkan 'yan takara a matakai daban-daban. A cewarsa, ɗan takarar gwamna zai biya Naira miliyan 150, ɗan takarar Sanata Naira miliyan 100, ɗan takarar Majalisar Wakilai Naira miliyan 50, yayin da ɗan takarar Majalisar Dokokin Jiha zai biya Naira miliyan 20. Darakta Janar na Ofishin Sadarwa na Gwamnatin Abia, Onyebuchi Ememanka, ya ce tsarin ba abin cece-kuce ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce tabbatar da tsaro, tsaftar muhalli da kuma gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsari. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta nuna bambanci ga kowace jam'iyya ko ɗan takara ba, muddin an bi ƙa'idoji kuma an biya kuɗin da aka tanada. Sai dai Ƙungiyar Masu Tallace-tallace ta Waje ta Najeriya (OAAN) ta nuna damuwa kan sabon jadawalin kuɗin, tana mai cewa kuɗaɗen sun yi tsauri kuma za su iya kawo cikas ga tallan siyasa a jihar. Shi ma shugaban jam'iyyar ADC a Abia, Kalu Kalu, ya ce idan dokar jihar ta tanadi irin waɗannan kuɗaɗe jam'iyyarsa za ta biya. Amma idan ba haka ba ne, ya kamata a soke tsarin. Ya kuma yi nuni da cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya bai wa ƙananan hukumomi ikon karɓar irin waɗannan kuɗaɗe, yana mai gargadin cewa duk wata doka da ta saɓa wa Dokar Zaɓe ba za ta dore ba.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img