Biza Da Fasfo: Amurka Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Amfani da Hotunan Fasfo da AI Ta Gyara

Amurka Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Amfani da Hotunan Fasfo da AI Ta Gyara wajen Fasfo Ko Neman Biza

Daga Wakiliya

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya gargadi masu neman biza da fasfo da su guji amfani da hotunan da aka gyara da fasahar Artificial Intelligence (AI) ko wasu kayan aikin gyaran hoto, yana mai cewa ba za a karɓi irin waɗannan hotuna ba.

A cikin wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, ya bayyana cewa dole ne hoton fasfo ya kasance na gaskiya, na kwanan nan, kuma ya yi daidai da kamannin mai nema a halin yanzu.

Sanarwar ta ce kada masu neman biza ko fasfo su yi amfani da AI, filtoci (filters), ko wani nau’in gyaran hoto na dijital yayin ɗaukar hoton fasfo.

Ofishin ya kuma jaddada cewa hoton dole ne ya kasance an ɗauke shi cikin watanni shida da suka gabata, domin jami’an tsaron kan iyaka da na filayen jiragen saman Amurka su iya gane mai hoton cikin sauƙi.

Haka kuma, ya yi gargadin cewa amfani da hoton da aka gyara ta hanyar dijital zai iya jinkirta aikin duba da amincewa da buƙatar fasfo ko biza.

Ofishin ya shawarci masu neman takardun tafiya zuwa Amurka su bi ƙa’idojin ɗaukar hoton fasfo da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tanada domin kauce wa matsaloli yayin gudanar da aikace-aikacensu.

DA DUMI-DUMI

Kotu a Rasha Ta Kwace Kadarori 123 Mallakin Ƙungiyar Kiristoci ta Jehovah’s Witnesses

Sai dai a shekarar 2022, Kotun Kare Haƙƙin Bil Adama ta Turai ta yanke hukuncin cewa haramta ƙungiyar ya saɓa wa doka.

KO KUN SAN? Hadiza Miller, Matar da Ta Wakilci Zariya a Majalisar Dokokin Kaduna a 1983

Hajiya Hadiza Miller ita ce 'yar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ta wakilci mazabar Zariya a shekarar 1983, a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus Ko Ta Tsige Shi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) Ta Bukaci Shugaban FIFA, Gianni Infantino Ya Yi Murabus, Akwai Shakku A Shugabancinsa

Barayi Sun Kutsa Makarantar Gwamnati a Jigawa Sun Yi Wa Masu Gadi Duka Sun Sace Kayan Wutan Lantarkin Makarantar

Hakazalika, ya buƙaci masu gadi da jami'an tsaro da ke kula da makarantu da sauran cibiyoyin gwamnati su ƙara sanya ido, sannan ya yi kira ga al'umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ɓarna a jihar.

TSOKACI: Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Dambarwar Waƙar Rarara: Lokaci Ya Yi da Za a Tsabtace Siyasar Zambo da Cin Mutunci

Kanun Labarai

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Duk Abin da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tallafin Dubu N50,000 na Gwamnatin Tarayya da Yadda Ake Nema

Rundunar sojin Indiya ta taba tilasta wa masu neman Soja rubuta jarabawa daga su sai dan kamfe don gudun satar jarabawa

A shekarar 2016, rundunar sojin Indiya ta tilasta wa sama da mutum 1,150 da ke rubuta jarabawar ɗaukar sojoji a jihar Bihar su cire dukkan tufafinsu, sai dai kayan ciki (underwear) kaɗai.

Remi Tinubu Ta Shawarci Matasan Najeriya Su Koyi Wadatar Zuci, Su Guji Kwaɗayi da Maular Abin Hannun Wasu

"Ku koyi gamsuwa da abin da kuke da shi, kada ku zama masu kwaɗayi ko roƙon abin hannun wasu," in ji ta.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img