Muslim-Muslim: Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta nemi a kama Sheikh Jingir
Daga Wakiliya
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kama tare da gurfanar da Sheikh Sani Yahaya Jingir bisa zargin yin kalaman ƙiyayya da tunzura jama'a.
Hukumar ta yi wannan kiran ne ganin yadda ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Hukumar, Chief Tony Ojukwu, SAN, ya sanya wa hannu ranar Talata, NHRC ta ce ta yi Allah-wadai da wasu kalamai da ta ce malamin ya yi a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ranar Lahadi.

Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin “tsananin damuwa”, tana mai cewa Sheikh Jingir ya yi kira ga tsarin siyasa da ya keɓe wasu mutane bisa addininsu, sannan ya yi amfani da kalmar “kafirai” yayin da yake kira ga magoya bayansa su mallaki katin zaɓe domin “nuna musu iyakarsu”.
NHRC ta bayyana cewa irin waɗannan kalamai sun saɓa wa ƙa'idojin da suka shafi daidaito, rashin nuna bambanci da zaman lafiya tsakanin al'ummar ƙasa, waɗanda kundin tsarin mulkin Najeriya da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa kan haƙƙin ɗan Adam suka tanada.
Hukumar ta ce tana kallon kalaman a matsayin zage-zage na ƙiyayya da tunzura jama'a bisa addini, tana mai gargadin cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da rikici a lokacin da ƙasar ke shirin shiga zaɓen 2027.
NHRC ta kuma yi kira ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Darakta Janar na Hukumar DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kama Sheikh Jingir tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Hukumar ta bukaci malaman addini, sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da su guji kalaman da za su iya raba kan al'umma.
Ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji siyasar da ta dogara da addini ko ƙabila, su mayar da hankali wajen tantance ‘yan takara bisa cancanta, ayyukan da suka yi wa al'umma da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam.
NHRC ta ce bai kamata a yi wa wani sassauci ba wajen gurfanar da masu irin waɗannan kalamai, ba tare da la'akari da matsayinsu ko jam'iyyar siyasar da suke tare da ita ba.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan lamarin tare da aiki da hukumomin tsaro, INEC da ƙungiyoyin fararen hula domin tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin zaman lafiya, ba tare da kalaman ƙiyayya da tashin hankali ba.