Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in jihar Kano
Daga Wakiliya
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ƙarin albashi ga malaman jami’a da sauran ma’aikatan jami’o’in Aliko Dangote University of Science and Technology da ke Wudil, da Northwest University da ke Kano.
Gwamnatin jihar ta ce sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in gwamnatin tarayya.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin, sabon tsarin zai fara aiki daga watan Janairun 2026, yayin da za a fara biyan albashin daga watan Satumban 2026.
Gwamnatin jihar ta ce ƙarin albashin zai jawo mata ƙarin kashe kuɗi naira miliyan 391.8 a kowane wata, wato sama da naira biliyan 4.7 a shekara, ga jami’o’in biyu.
A jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, ƙarin kuɗin zai kai kusan naira miliyan 228.2 a wata. Daga cikin wannan kuɗin, naira miliyan 141.1 za a kashe wajen ma’aikatan koyarwa, yayin da kusan naira miliyan 87.1 za a kashe wajen ma’aikatan da ba na koyarwa ba.
A Northwest University kuwa, gwamnatin jihar ta ce ƙarin kuɗin zai kai kusan naira miliyan 163.7 a wata, wanda ya haɗa da naira miliyan 112.2 ga malaman jami’a da naira miliyan 51.4 ga sauran ma’aikata.
Sanarwar ta ce gwamnatin Kano ta ware sama da naira biliyan 1.56 a kasafin kuɗin ƙarin shekarar 2026 domin biyan kuɗin daga Satumba zuwa Disamba.
Haka kuma, za a tanadi sama da naira biliyan 3.13 a kasafin kuɗin shekarar 2027 domin biyan bashin ƙarin albashin da ya shafi watan Janairu zuwa Agusta 2026.
Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ma’aikata, tare da inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’in.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.
Gwamnatin ta ce inganta jin daɗin ma’aikata da kuma bunƙasa ilimin gaba da sakandare na daga cikin manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na zuba jari a harkar bunƙasa ɗan Adam.





