Atiku, Obi, Kwankwaso da Makinde za su gana a Abuja domin duba yiwuwar dunƙulewa su marawa mutum ɗaya a 2027

Atiku, Obi, Kwankwaso da Makinde za su gana a Abuja domin duba yiwuwar dunƙulewa su marawa mutum ɗaya a 2027

Daga Wakiliya

Ƙungiyar G100 da ke ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyun adawa a Najeriya ta ce ta shirya wani taron shugabannin adawa da za a gudanar a Abuja ranar 18 ga Agusta, 2026.

Ƙungiyar ta ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi wajen samar da babbar ƙawancen jam’iyyun adawa domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cikin wata sanarwa da Salihu Lukman ya fitar, G100 ta ce ta riga ta gudanar da shawarwari na sirri da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na NDC, da kuma wakilan Seyi Makinde na APM, PDP, PRP da SDP.

Ta ce tattaunawar da aka yi da shugabannin jam’iyyu, ‘yan takarar shugaban ƙasa da abokan takararsu ta kasance cikin gaskiya da nufin samar da mafita, ba tare da kutsawa cikin kafafen yaɗa labarai ba.

A cewar G100, mahalarta tattaunawar sun amince cewa samar da ingantacciyar adawa na buƙatar sadaukar da kai da kuma fifita muradun ƙasa a kan burin mutum.

Ƙungiyar ta ce rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa ba ta amfani ga ‘yan siyasar adawa ko al’ummar Najeriya.

Sai dai G100 ta jaddada cewa ba ta da niyyar tilasta wa jam’iyyun wani matsaya, illa dai samar da hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Taron na ranar 18 ga Agusta zai mayar da hankali kan “Doctrine of Necessary Democratic Opposition”, wato tsarin da ƙungiyar ta ce zai taimaka wajen samar da haɗin kan adawa mai ƙarfi.

DA DUMI-DUMI

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in jihar Kano

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu -Aregbesola

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.

SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Shan ruwan ’ya’yan itace (smoothie) a kullum na iya rage cutar damuwa (depression) – bincike

Saboda haka, suna ganin akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko shan ruwan ’ya’yan itace a kai a kai na da tasiri kai tsaye wajen rage alamun damuwa. Binciken an wallafa shi a mujallar British Journal of Nutrition, kuma Fruit Juice Science Centre ce ta ɗauki nauyin gudanar da shi.

Kanun Labarai

Da kafa Tinubu ke zuwa ofis, kuma sau ɗaya yake cin abinci a rana – Shugaban NRS, Zacch Adedeji

Kan yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da hukumomi da ma’aikatu, shugaban NRS ya ce bai kamata a rika kallon kuɗin da gwamnati ke kashewa kawai ba, domin akwai kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da kuma kuɗaɗen da take samarwa ta hanyar waɗannan ayyukan.

Nazari: Yadda rashin tsaro ke kara jefa yaran Arewa cikin matsalar rashin zuwa makaranta

Ya kuma yi gargadin cewa yaran da ba sa makaranta na iya zama masu saukin fadawa hannun kungiyoyin 'yan ta'adda, 'yan bindiga da sauran kungiyoyin aikata laifuka.

Babu gaskiya a labarin cewa Sarki Sanusi ya samu ‘carry over’ — Masarautar Kano

Masarautar ta kuma ce bidiyon da ake yaɗawa an dauke shi ne yayin wani shiri da ɗaliban Shari’a suka gudanar, inda wasu matasa suka shirya shi da nufin yaɗa bayanan ƙarya.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img