Gumi ya gargadi Sheikh Jingir, amma ya ce a yi wa malamin uzuri: “Ya taso ne a Plateau, jihar da ake tsananin nuna ƙiyayya ga Musulunci”

Daga Wakiliya

Malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga Sheikh Sani Yahaya Jingir da ya guji shigar da addini cikin siyasar jam’iyyu.

Dr Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a Facebook ranar Litinin, bayan Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kare tsarin tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC, tare da kira ga Musulmi da su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ya zaɓi Musulmi a matsayin mataimakinsa.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi wannan magana ne a wani taron bikin auren gata da aka gudanar a Kano ranar Asabar.

Sai dai Dr Ahmad Gumi ya ce a ƙasar da ke da addinai daban-daban, bai kamata a jawo addini cikin siyasar da ke cike da rikici ba.

“A cikin ƙasa mai addinai da dama, bai kamata a jawo addini cikin rikitaccen siyasar da ke cike da kazanta ba,” in ji Dr Ahmad Gumi.

Ya kuma ce ya kamata a yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir uzuri saboda matsanancin ra’ayinsa, yana mai cewa malamin ya taso a jihar Plateau inda suke fuskantar abin da ya kira “tsananin nuna ƙiyayya ga Musulunci”.

Dr Ahmad Gumi ya ƙara da cewa ko ɓangaren adawa ma bai kamata su rika amfani da addini ba wajen harkokin siyasa inda ya wallafa bidiyon Peter Obi dan takarar Jam'iyyar NDC da aka nuna shi yana kalaman addinanci a coci.

DA DUMI-DUMI

An sauya jirgin Trump a asirce saboda tsoron barazanar Iran

Rahoton ya ce Trump ya fito fili ya hau Air Force One, amma daga baya aka fitar da shi a asirce ta hanyar wata motar ɗaukar kayan abinci, aka kai shi wani ƙaramin jirgin soji kirar C-32A.

Muslim-Muslim: Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta nemi a kama Sheikh Jingir

Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin "tsananin damuwa", tana mai cewa Sheikh Jingir ya yi kira ga tsarin siyasa da ya keɓe wasu mutane bisa addininsu, sannan ya yi amfani da kalmar "kafirai" yayin da yake kira ga magoya bayansa su mallaki katin zaɓe domin "nuna musu iyakarsu".

Muslim-Muslim: Idan Tinubu ya iya karanta Suratul Fatiha daidai, zan zaɓe shi-  MC Tagwaye ya ƙalubalanci Jingir

Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wasu kalamai da aka danganta ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta.

Atiku, Obi, Kwankwaso da Makinde za su gana a Abuja domin duba yiwuwar dunƙulewa su marawa mutum ɗaya a 2027

G100 ta ce ta riga ta gudanar da shawarwari na sirri da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na NDC, da kuma wakilan Seyi Makinde na APM, PDP, PRP da SDP.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in jihar Kano

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙara inganta sa ido, shugabanci da yadda ake tafiyar da cibiyoyin ilimi.

Kanun Labarai

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu -Aregbesola

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin ADC a Ejigbo, Jihar Osun, inda ya ce tsoron Allah da kuma sadaukarwarsa ga aurensa ne suka sa ya kasance mai aminci.

SOKOTO: An rufe makarantu a kananan hukumomi 20 saboda rashin tsaro

Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantu ta All Nigerian Conference of Principals of Secondary Schools, Muhammad Ikililu, ya ce rashin tsaro ya dade yana kawo cikas ga tsarin makarantun kwana a jihar.

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img