Shan kofin ruwan ’ya’yan itace (smoothie) a kullum na iya rage cutar damuwa (depression) – bincike
Daga Wakiliya
Wani sabon bincike daga Jami’ar Newcastle da ke Birtaniya ya nuna cewa shan gilashin ruwan ’ya’yan itace 100% ko smoothie a kullum na iya taimakawa wajen inganta lafiyar kwakwalwa da rage alamun damuwa.
Binciken ya shafi manya 42 da suka kasance suna cin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu kaɗan, wato guda biyu ko ƙasa da haka a rana.
An raba mahalarta zuwa rukunoni uku. Wasu sun ci gaba da tsarin abincinsu na yau da kullum, yayin da wasu aka ba su shawarwari da tallafin kuɗi domin su ƙara yawan ’ya’yan itatuwa da kayan lambu har su kai guda biyar a rana.
Rukuni na uku kuma sun ƙara gilashin ruwan ’ya’yan itace ko smoothie guda ɗaya a kowace rana, tare da cin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu.
Bayan makonni huɗu, masu binciken sun gano cewa mutanen da suka sha ruwan ’ya’yan itace ko smoothie sun samu raguwar alamun damuwa fiye da rukunin da ba su yi wannan ƙarin ba.
A ma’aunin da aka yi amfani da shi, maki na alamun damuwa sun ragu da kusan 2.52 cikin 27.
Masu binciken sun ce wannan bambancin ba babba ba ne, amma yana da muhimmanci a kididdiga kuma yana buƙatar ƙarin bincike.
Ƙarin sinadarin fiber
Binciken ya kuma nuna cewa rukunin da aka ƙarfafa su su ƙara cin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu sun ƙara yawan sinadarin fiber da suke samu daga abinci.
An kiyasta cewa yawan fiber ɗin da suke ci ya ƙaru da gram 8 zuwa 10 a rana.
Masu binciken sun ce wannan na nuna cewa ƙara ruwan ’ya’yan itace ko smoothie bai hana mahalarta ƙara cin abincin da ke ɗauke da fiber ba.
Binciken bai kuma gano wata illa ga wasu alamomin lafiyar jiki da suka shafi narkewar abinci ko sukari a jini ba bayan makonni huɗu.
Me binciken ya gano?
Dokar cin abinci ta Birtaniya ta ƙarfafa mutane su ci aƙalla nau'o'in ’ya’yan itatuwa da kayan lambu guda biyar a rana.
Sai dai bayanai sun nuna cewa mutane da dama ba sa kai wannan adadin.
Masu binciken sun ce shan ƙaramin gilashin ruwan ’ya’yan itace 100% ko smoothie na iya zama wata hanya mai sauƙi ta taimaka wa mutane wajen ƙara yawan ’ya’yan itatuwa da kayan lambu da suke samu a rana.
Dr Courtney Neal, wadda ta gudanar da binciken a Jami’ar Newcastle, ta ce mutane da dama suna samun wahalar kai wa matakin guda biyar a rana, duk da cewa suna sane da amfanin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu.
Ta ce binciken ya nuna cewa tallafin kuɗi da ilimi na iya taimaka wa mutane su canza tsarin cin abincinsu.
Sai dai masu binciken sun jaddada cewa binciken ƙarami ne, domin mutane 42 ne kawai suka shiga, kuma an gudanar da shi tsawon makonni huɗu.
Saboda haka, suna ganin akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko shan ruwan ’ya’yan itace a kai a kai na da tasiri kai tsaye wajen rage alamun damuwa.
Binciken an wallafa shi a mujallar British Journal of Nutrition, kuma Fruit Juice Science Centre ce ta ɗauki nauyin gudanar da shi.





