Yanzu na ga an rage yi min maganan aure, ina ga sun gaji ne -DJ AB

DA DUMI-DUMI

Fitaccen mawakin Hausa, DJ AB, ya jawo hankalin mabiyansa bayan ya wallafa sakonni biyu masu ɗauke da barkwanci a shafukansa na sada zumunta.

A sakon farko, mawakin ya yi tsokaci kan yawan tambayoyin da ake masa game da aure, inda ya rubuta:

“Yanzu na ga an rage min maganan aure, ina ga sun gaji ne.”

Daga baya kuma, ya sake wallafa wani sako yana barkwanci kan tumbinsa, yana cewa:

“Nan da December za ku nemi tumbi na ku rasa.”

Sakonnin biyu sun jawo martani daga mabiyansa, inda wasu suka yi ta raha a kan batun aure, yayin da wasu kuma suka ce za su jira su ga ko DJ AB zai cika alkawarinsa na kawar da tumbinsa kafin watan Disamba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img