Bashir Ahmad ya musanta yin ƙorafi kan gwamnatin Tinubu ga Bello El-Rufai – Kuma ya kalubalance shi ya kawo hujja
Daga Wakiliya
Tsohon mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad, ya musanta cewa ya taɓa yin ƙorafi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a wata tattaunawa da Bello El-Rufai.
Bashir ya yi wannan bayani ne bayan wani rubutu da Bello El-Rufai ya yi a Facebook, inda ya mayar da martani ga wani rubutun Bashir da ya ce: “Za mu sake zaɓar Tinubu.”
A martanin da Bello ya yi, ya ce: “Sai ka zaɓe shi. Kani na. Ama last time mu ka hadu. Ka yi complain. You don’t need to announce it. Ka riƙe akwatin ka.”
Sai dai Bashir ya ce ya yi mamakin kalaman Bello, inda ya bayyana cewa bai tuna sun taɓa tattauna batun gwamnatin Tinubu, zaɓe ko wani abu makamancin haka ba.
Ya ce ya tambayi Bello kai tsaye inda ya yi wannan ƙorafin da kuma abin da ya ƙorafa a kai.
Bashir ya ce: “Ban yi wa Bello wani ƙorafi game da Shugaba Tinubu ko gwamnatinsa ba.”
Ya kuma bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar APC, mai goyon bayan Shugaba Tinubu kuma mai yaƙin neman sake zaɓensa.
Sai dai Bashir ya ce kowane ɗan Najeriya na da ’yancin sauya matsayinsa na siyasa idan ya daina gamsuwa da shugabanci ko manufofin wata gwamnati ko jam’iyya.
Ya ƙara da cewa ba ya goyon bayan anti-party, kuma matuƙar yana cikin APC, zai ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu.
Bashir ya buƙaci Bello El-Rufai, idan akwai wata takamaiman magana ko tattaunawa da yake nufi, da ya fito da ita tare da cikakken bayanin yadda aka yi ta.
Ya ce hakan zai taimaka wajen kawar da rashin fahimta, musamman ganin yadda rubutun Bello ya janyo masa martani da kalaman cin mutunci daga wasu masu amfani da shafukan sada zumunta.




