“Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” – Tinubu

DA DUMI-DUMI

DA DUMI-DUMI: “Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” – Tinubu

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce kasar ta kammala wani muhimmin mataki na gyaran tattalin arziki, kuma yanzu lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan samar da wadata ga ‘yan kasa.

A cikin jawabin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai, Tinubu ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar sun kasance masu wahala, amma sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba da sama da kashi 4 cikin 100 a bana, yayin da hauhawar farashi ta ragu daga kololuwarta, sannan ajiyar kudaden waje da kasuwar musayar kudin kasar suka samu sauki.

Shugaban ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa, bunkasa noma da masana’antu, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta ababen more rayuwa.

Tinubu ya ce ya san wasu na fama da talauci har ma abincin ci yana gagararsu amma matsalar ba ta fara da gwamnatina ba “Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” Wahalar da ’yan Najeriya ke ciki ta samo asali ne daga shekaru da dama kuma ba za mu iya kawar da matsalar da ta taru shekaru da dama cikin shekaru huɗu ba”

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img