“Idan kika mutu ba tare da kin taɓa samun inzali ba, kin yi rayuwa a banza” – Fasto ta shawarci mata

DA DUMI-DUMI

TABDIJAN: “Idan kika mutu ba tare da kin taɓa samun inzali ba, kin yi rayuwa a banza” – Fasto ta shawarci matan aure

Daga Ayau News

Wata fasto, Mummy Owolabi, ta shawarci matan aure da su ƙara fahimtar zamantakewar aure da kuma jin daɗin kusancin da ke tsakaninsu da mazajensu.

Fasto Mrs Owolabi, ta bayyana hakan ne yayin wani shiri mai suna Marriage That Works, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar aure.

Ta ce bai kamata mata su ɗauki jima’i a matsayin hanyar haihuwa kawai ba, tana mai cewa Allah ne ya halicci jima’i kuma ya tsara shi a cikin aure.

“Idan kika mutu ba tare da kin taɓa samun inzali ba, kin yi rayuwa a banza,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa mata suna da haƙƙin fahimtar yadda za su more kusancin aure, tare da koyon abubuwan da suka shafi rayuwar jima’i.

Ta kuma shawarci matan aure da su ƙara neman ilimi kan yadda za su inganta kusancin aure, tana mai cewa babu laifi ma’aurata su gwada wasu hanyoyin kusanci (saduwa) daban-daban a cikin aure.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img