Mun San Abin Da Aka Shirya Mana a Mile 3 a hanyar dawowar mu Gombe -Pantami 

DA DUMI-DUMI

Mun San Abin Da Aka Shirya Mana a Mile 3 a hanyar dawowar mu Gombe -Pantami

Daga Wakiliya

Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa an shirya masa wani “mummunan shiri” a yankin Mile 3 da ke kan hanyar dawowarsa Gombe daga Kaltungo, Billiri da Shongom, inda ya je gaisuwar ta’aziyya.

Pantami ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa, inda ya ce sun samu labarin abin da yake zargin an shirya musu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Gombe.

Ya ce sakon da yake da shi ga wadanda ya ke zargin suna da hannu a shirin a bayyane yake, yana mai kafa hujja da ayar Al-Qur’ani:

“Suna kulla makirci, Allah ma yana kulla tsari, kuma Allah ne Mafi kyawun masu tsara makirci.” – Al-Qur’ani 8:30.

Pantami bai bayyana cikakken bayani kan abin da ya kira “mummunan shiri” ko wadanda yake zargin suna da hannu a ciki ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img