Gwamnonin APC sun ki amincewa da tsarin shinkafa da wake wato “Rainbow Coalition” da Wike ya fito da shi
Daga Wakiliya
Wasu shugabannin jam’iyyar APC a jihohin Najeriya sun yi watsi da kawancen siyasar da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta, inda suka bukaci ya shiga APC idan da gaske yake son goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce Wike ba zai iya kasancewa a PDP a lokaci guda yana goyon bayan APC ba.
Ya ce: “Ko dai ya shiga APC ko kuma ya fita.”
Shugabannin APC na Imo, Gombe, Ondo, Kwara, Plateau da Nasarawa sun bayyana irin wannan matsaya, yayin da wasu jihohi kamar Jigawa suka ce za su yi maraba da Wike idan ya yanke shawarar shiga APC.
Sai dai Wike ya dage cewa kawancen nasa ba na APC ba ne, kuma manufarsa ita ce kawai tabbatar da sake zaben Tinubu a 2027.
Wike ya kuma ce “siyasa ta gida ce”, don haka ya kamata ‘yan siyasa su samu damar yin kawance da jam’iyyu daban-daban a matakin jiha wato ayi shinkafa da wake.




