Ku Guji Waƙoƙin Turanci na Afrobeats, Suna Lalata Tarbiyyar Matasa -Fasto Paul Enenche
Daga Wakiliya
Babban Faston cocin Dunamis International Gospel Centre, Dr. Paul Enenche, ya soki salon waƙoƙin turanci na Afrobeats, yana mai cewa yawancin waƙoƙin ba sa ɗauke da saƙo mai amfani, kuma suna yin mummunan tasiri ga matasa.
Da yake jawabi a taron ibadar tsakiyar shekara na cocinsa, Dr. Paul Enenche ya ce wasu daga cikin mawaƙan Afrobeats suna rera “waƙoƙin banza ne”, tare da zargin cewa wasu na shan miyagun ƙwayoyi yayin da suke waƙa, abin da ya ce yana jawo matasa zuwa munanan ɗabi’u.
Ya buƙaci mawaƙan waƙoƙin bishara su ƙara fitar da waƙoƙin da za su ja hankalin matasa, domin su maye gurbin abin da ya bayyana a matsayin mummunan tasirin waƙoƙin duniya.
A cewarsa, waƙoƙin bishara masu ƙunshe da saƙonni masu amfani za su taimaka wajen koyar da matasa yadda za su guji abokan banza, su yanke shawara mai kyau, da kuma rayuwa bisa kyawawan ɗabi’u.





