Mun fara tattaunawa da Jam’iyyun Adawa don hada karfi waje guda mu kawar da Tinubu – Dr. Hakeem
Daga Wakiliya
Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyar ta fara tuntubar shugabanni da ‘yan takarar jam’iyyun adawa domin samar da haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027.
Baba-Ahmed ya bayyana cewa sun fara da ziyarar Wazirin Adamawa, ɗan takarar ADC, da shugabannin jam’iyyar, sannan za su gana da ɗan takarar NDC da shugabannin jam’iyyar.
Ya ce PRP za ta tattauna da duk jam’iyyar da ke da sha’awar haɗa ƙarfi domin kalubalantar gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Baba-Ahmed ya ce burinsu shi ne haɗa ƙarfin jam’iyyun adawa da neman goyon bayan jama’a domin kawo sauyi a Najeriya ta hanyar kawar da Tinubu a zaben 2027.




