Yaro Ya Rasu Bayan Mahaifiyarsa Ta Rasa Samun N3,000 Na Magani – Dr. Zainab

DA DUMI-DUMI

Likita Ta Bayyana Hanyoyi 12 Da Za A Gyara Matsalolin Lafiyar Najeriya

Wata ma’aikaciyar lafiya, Dr Zainab Suleiman Buhari, ta bayyana hanyoyi 12 da take ganin za su taimaka wajen gyara matsalolin tsarin kiwon lafiya a Najeriya.

Dr Zainab ta ce ta taba ganin wata uwa tana neman N3,000 na maganin ɗanta da ke fama da farfaɗiya, amma yaron ya rasu, lamarin da ta ce ya hana ta barci.

Daga cikin abubuwan da ta gabatar akwai samar da tsarin ganin gadojin asibiti ta yanar gizo, inganta sashen gaggawa (A&E), tsaftar asibitoci, da samar da ingantattun dakunan tiyata.

Ta kuma bukaci a samar da magunguna kyauta ga yara masu cututtukan jijiyoyi, tare da tallafa wa masu fama da sickle cell, hawan jini, ciwon sukari da hepatitis.

Dr Zainab ta kuma gabatar da ra’ayin kafa sashen aikin jarida mai binciken harkokin lafiya, wanda zai rika binciken asibitoci, shagunan magani da masu sayar da magunguna domin gano abubuwan da ke jefa rayukan jama’a cikin hadari.

Ta ce ya kamata a hada irin wannan aiki da hukumomi irin su NAFDAC, SON, FCCPC da Pharmacists Council of Nigeria domin tabbatar da ingancin magunguna da ayyukan kiwon lafiya.

Ta kara da cewa ya kamata a inganta albashin ma’aikatan lafiya, a kara musu alawus-alawus, tare da kafa cibiyar bincike domin samar da magunguna da alluran rigakafi a Najeriya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img