APC na neman kuri’un mata miliyan 40 domin sake zaɓen Tinubu a 2027
Daga Wakiliya
Jam’iyyar APC ta ce tana sa ran samun kuri’un mata miliyan 40 domin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaɓen 2027.
Daraktar Yaƙin Neman Zaɓen Mata ta APC, Dr Betta Edu, ce ta bayyana hakan gabanin taron mata masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da za a gudanar a Abuja ranar Litinin.
Ta ce taron, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, za ta jagoranta, zai ƙara ƙarfafa tsarin janyo hankalin mata a faɗin ƙasar.
Betta Edu ta ce APC ta fara tuntuɓar mata da gidaje a matakin ƙasa, inda tsarin wayar da kan jama’a ya shafi al’ummomi 176,846 a faɗin Najeriya.
Ta ce: “Tsere ne na kwanaki 100, kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai an samu nasara ga Shugaba Tinubu.”




