“Jika na yaƙi yarda ya yi aiki a karkashi na” – Dangote
Daga Wakiliya
Shahararren ɗan kasuwa kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce babban jikansa ya ce ba ya sha’awar fara aiki da shi a halin yanzu.
Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron masu zuba jari da aka gudanar a Nairobi, Kenya, kan sayar da hannun jarin matatar Dangote.
Ya ce jikansa, wanda injiniyan lantarki ne, yana son fara samun ƙwarewa a fannin kuɗi a kamfanonin ƙwararrun harkokin kasuwanci na duniya, KPMG ko PwC, kafin daga bisani ya shiga kasuwancin kakan nasa.
“Jikana na farko ba ya ganin aiki da ni yana da armashi a yanzu. Yana son ya je KPMG ko PwC ya samu ƙwarewa, daga nan zai dawo ya shiga kamfaninmu,” in ji Dangote.
Dangote ya kuma ce ’ya’yansa mata uku, Mariya, Halima da Fatima, sun riga sun rike manyan mukamai a cikin rukunin kamfanonin Dangote.
Ya ce bai damu da samun ɗa namiji da zai gaji harkokin kasuwancinsa ba, domin yana da yakinin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata za ta iya jagorantar kamfanin a nan gaba.




