Mutane 25 sun mutu a hatsarin jirgin saman Sojojin Najeriya a Ondo – kalli sunayen su
Daga Wakiliya
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 25 da ke cikin wani jirgin soji da ya yi hatsari a yankin Igbokoda na jihar Ondo.
Jirgin mai lamba NAF 931, kirar ATR 42, na dauke da ma’aikata biyar da fasinjoji 20 lokacin da hatsarin ya afku.
Rundunar ta ce jirgin yana kan hanyarsa ne daga Benin zuwa Legas a wani aikin yau da kullum.
An fara aikin ceto nan take bayan hatsarin, amma rundunar ta ce ba a samu wani mai rai ba daga cikin mutanen da ke cikin jirgin.
Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su guji yada jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Ga sunayen wadanda suka mutu:
-
Squadron Leader MI Aburime
-
Squadron Leader AP Man-Ugwueje
-
Flight Lieutenant IS Bako
-
Warrant Officer Abubakar A
-
Corporal Uguru HC
-
Flight Lieutenant TL Lazarus
-
Flight Lieutenant M Akinloye
-
Flying Officer IM Adeshina
-
Master Warrant Officer Onwuka F
-
Master Warrant Officer Matini BA
-
Warrant Officer Nuhu FS
-
Flight Sergeant James RB
-
Flight Sergeant Mohammed AI
-
Sergeant Ani AE
-
Sergeant Izibenikien SI
-
Sergeant Alafuka C
-
Sergeant Mbadugha AN
-
Lance Corporal Ugwuba FC
-
Lance Corporal Eledan GE
-
Mrs Ezeh Nneka
-
Godstmine Tarabina
-
Joy Micheal
-
Sunday Micheal
-
Ukeme David
-
Gideon Omotola




