Gwamna Uba Sani, ya bayar da umarnin cire duk wasu fastoci da allunan tallan ’yan takarar APC da basu da hoton Tinubu

DA DUMI-DUMI

Gwamna Uba Sani, ya bayar da umarnin cire duk wasu fastoci da allunan tallan ’yan takarar APC da basu da hoton Tinubu

Daga Wakiliya

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayar da umarnin cire duk wasu fastoci da allunan tallan ’yan takarar jam’iyyar APC da ba su ƙunshi hoton Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba.

Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Najeriya, ALGON, Jamilu Albani, ne ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

Albani ya ce ya kafa wani allon talla da ke ɗauke da hotonsa da na Gwamna Uba Sani, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryensa na neman takara a zaɓen 2027.

Sai dai ya ce hukumomin kula da muhalli na jihar Kaduna sun rushe allon tallar tare da cire shi.

Ya ce bayan ya gudanar da bincike domin gano dalilin cire tallar, shugaban hukumar ya sanar da shi cewa umarnin ya fito ne daga Gwamna Uba Sani.

A cewar Albani, umarnin ya tanadi cewa duk wani poster ko billboard da ke tallata ’yan takarar APC a Kaduna dole ne ya kasance da hoton Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img