Shettima ya nemi ’yan Najeriya su yi wa Tinubu sassauci, bawan Allah ne

DA DUMI-DUMI

Shettima ya nemi ’yan Najeriya su yi wa Tinubu sassauci, bawan Allah ne

Daga Wakiliya

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya nemi ’yan Najeriya da su yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sassauci, suna la’akari da irin mawuyacin halin tattalin arzikin da gwamnati ta gada a shekarar 2023.

Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu tsauri, ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kudade, domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.

Ya ce lokacin da gwamnatin ta karbi mulki, ajiyar kudaden waje na Najeriya ya kai kusan dala biliyan 3.9, abin da ya ce bai isa a shigo da man fetur na wata guda ba.

“Ina ganin ya kamata ’yan Najeriya su yi wa wannan bawan Allah sassauci,” in ji Shettima yayin da yake magana kan Tinubu.

Mataimakin shugaban ya amince cewa sauye-sauyen sun jefa ’yan Najeriya cikin wahalhalu, amma ya ce matsalolin ba za su dore har abada ba.

“Lokuta masu wahala ba sa dawwama, amma mutane masu juriya sukan dawwama,” in ji shi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img