“Goyon bayan Tinubu ne ya janyo wannan cece-kucen; ra’ayina ne, ba na ƙorafi, ban sa kaina inda ba ni da daraja” – Bashir Ahmad

DA DUMI-DUMI

“Goyon bayan Tinubu da nake yi ne ya janyo wannan cece-kucen a kaina; ra’ayina ne, ba na yin ƙorafi, kuma ban sa kaina inda ba ni da daraja” – Bashir Ahmad ya mayar wa Ja’afar Ja’afar

Daga Wakiliya

Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad, ya mayar da martani ga marubuci kuma ɗan jarida Ja’afar Ja’afar, bayan Ja’afar ya yi tsokaci kan cece-kucen da ya biyo bayan wata magana tsakanin Bashir Ahmad da Bello El-Rufai.

Ja’afar ya bayyana cewa bai ga abin mamaki ba idan Bashir ya nuna rashin gamsuwa bayan ya yi wa ɗan siyasa kamfen, yana mai ba da labarin yadda shi kansa ya koma aikin jarida bayan gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta kammala wa’adinta a 2015.

Ya kuma ba Bashir shawarar cewa ya koma aikin jarida, ya kafa nasa kamfanin ko ya mayar da hankali kan harkokin kasuwanci, yana mai cewa bai kamata mutum ya matsa wa gwamnati ko jami’an gwamnati idan ba a nemi sa ba.

Sai dai Bashir ya ce Ja’afar ya yi wasu zato ne da ba su da tushe, domin ya sake jaddada cewa bai yi wa Bello El-Rufai wani ƙorafi ba a haduwarsu ta ƙarshe.

Bashir ya ce: “Ban yi wani ƙorafi ba a haduwarmu da shi ta ƙarshe. Don haka ban fahimci dalilin da ya sa har ka yi assuming irin kalar ƙorafin da na yi masa ba.”

Ya ƙara da cewa idan har yana da wani ƙorafi, ya san inda zai kai shi, kuma yana da yakinin za a saurare shi.

Game da maganar cewa an kafa gwamnati da shi sannan yake tsammanin wani abu, Bashir ya ce ba ya sanya kansa a inda ya san ba shi da daraja ko kuma ba a ganin mutuncinsa.

Bashir ya kuma ce goyon bayan da yake bai wa Shugaba Bola Tinubu a yanzu ra’ayinsa ne, kuma yana cikin ’yancinsa na siyasa ya bayyana wanda ya gamsu da shi.

Dangane da shawarar Ja’afar na komawa aikin jarida ko kasuwanci, Bashir ya gode masa, yana mai cewa shi ma yana da nasa kamfanin media kuma, bisa bayaninsa, kamfanin yana tafiya yadda ya kamata a Najeriya da wajen ƙasar.

Ya ce yana matuƙar godiya ga Allah kan abin da yake samu a rayuwarsa, tare da yi wa Ja’afar fatan samun ƙarin nasarori.

 

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img