Sabon kamfanin sadarwa mai suna STN ya samu lasisin fara aiki a Najeriy, zai yi gogayya da su MTN, GLO, Airtel DSS
Daga Wakiliya
Swift Telephone Network Limited (STN) ya samu lasisin fara aiki na UASL daga Gwamnatin Tarayya, wanda zai ba shi damar samar da ayyukan sadarwa a fadin Najeriya kamar yadda su GLO, MTN, Airtel da 9Mobile ko T2 ke yi.
Babban Daraktan kamfanin, Oluwole Adetuyi, ya ce kamfanin zai bayyana shirinsa na fara aiki da kuma abokan huldarsa a cikin makonni masu zuwa.
Daraktar Sashen Shari’a da Ka’idoji, Yetunde Okafor, ta ce burin kamfanin shi ne gina wata kafar sadarwa mai tushe a Najeriya wadda za ta yi gogayya a duniya.
Kuna nan a su MTN da Airtel da GLO ko za ku bi STN ?




