“El-Rufai Ya Yi Zaton Tsare Shi Zai Janyo Rikici a Arewa” – BKO Shugaban TVC

DA DUMI-DUMI

“El-Rufai Ya Yi Zaton Tsare Shi Zai Janyo Rikici a Arewa” – BKO Shugaban TVC

Daga Wakiliya

Fitaccen dan jarida kuma Daraktan Labarai na TVC News, Babajide Kolade-Otitoju, ya ce tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi tunanin tsare shi zai janyo gagarumar hayaniya ko zanga-zanga a Arewacin Najeriya.

Babajide Kolade-Otitoju, wanda aka fi sani da BKO, ya ce a maimakon haka, El-Rufai ya samu kansa cikin yanayi na kadaici, inda wasu daga cikin mutanen da ya taba taimakawa a siyasance suka yi watsi da shi suka yi shiru.

Da yake magana a shirin Issues With Jide na TVC News, BKO ya ce El-Rufai ya shafe sama da kwanaki 200 a tsare a hannun ICPC, yayin da sharuddan belinsa suka kasance masu wahalar cikawa.

Ya ce idan ba a sauya sharuddan belin ba, akwai yiwuwar tsohon gwamnan ya ci gaba da kasancewa a tsare har bayan zaben 2027.

BKO ya kuma ce wasu daga cikin shugabannin Arewa da mutanen da suka kasance kusa da El-Rufai a baya ba su fito fili suna magana kan lamarin ba.

A cewarsa, wannan yanayin na nuna yadda siyasa za ta iya sauya alakar mutane, musamman idan wani mutum ya samu kansa cikin rikici da hukumomin gwamnati.

El-Rufai na fuskantar shari’o’in da suka shafi zarge-zargen cin hanci da rashawa, yayin da ake ci gaba da muhawara kan tsawon lokacin da ya shafe a tsare da kuma sharuddan belinsa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img