ECOWAS Ta Buɗe Shirin Horo, Ɗaukar Aiki da Cikakken Tallafi Kyauta Ga Matasa Masu Digiri – Ga Yadda Za Ku Nema

ECOWAS Ta Buɗe Shirin Horo da Aiki Na Shekara Ɗaya Mai Cikakken Tallafi Ga Matasa Masu Digiri

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta buɗe neman gurbin shiga Shirin Horo da Aiki na Matasa Masu Digiri na 2027 (Young Graduates Immersion Programme).

Shirin zai bai wa matasa daga ƙasashen ECOWAS, ciki har da Najeriya, damar yin aiki na tsawon shekara guda a cibiyoyi da hukumomin ECOWAS tare da cikakken tallafi.

Waɗanda za su iya nema

Domin samun damar shiga shirin, dole ne mai nema ya:

  • Kasance ɗan ƙasar da ke cikin ECOWAS, ciki har da Najeriya.

  • Ya kasance bai wuce shekara 32 ba.

  • Ya mallaki takardar digiri daga jami’a ko wata cibiyar ilimi da aka amince da ita.

Yaushe za a rufe neman?

An fara karɓar buƙatu ne daga 31 ga Yuli, 2026, kuma za a rufe ranar 31 ga Agusta, 2026.

Yadda ake neman

Masu sha’awa za su shiga shafin neman gurbin na ECOWAS domin cike fom ɗin neman shiga.

Za a buƙaci su:

  • Ƙirƙiri asusu.
  • Cike bayanan kansu da na tuntuɓa.

  • Shigar da bayanan karatu da ƙwarewa.

  • Loda takardar digiri, CV da wasiƙar bayyana dalilin neman gurbin (Motivation Letter).

  • Duba bayanan da suka cike.

  • Aika buƙatar bayan sun tabbatar da komai.

Abin da waɗanda aka zaɓa za su samu

Waɗanda suka yi nasara za su yi aiki na shekara guda a hukumomin ECOWAS, inda za su:

  • Samu ƙwarewar aiki a cibiyoyin ECOWAS.
  • Samu horo na musamman da jagoranci daga ƙwararru.

  • Haɓaka ƙwarewar shugabanci.

  • Gina alaƙa da ƙwararru daga ƙasashen Afirka da sauran duniya.

ECOWAS ta ce manufar shirin ita ce haɓaka matasa masu ilimi tare da ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ƙasashen Yammacin Afirka.

DA DUMI-DUMI

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.

Wani Mutum da ‘Yan Sanda Suka Baza Hotonsa Suna Nemansa Ruwa a Jallo Ya Sake Aika Musu Sabon Hoto, Ya Ce Wanda Suka Saka...

"Ga hoto na mai kyau ku canza. Wanda kuka saka ba ya min kyau kwata-kwata."

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

Kanun Labarai

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al'adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma 'yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya," in ji ta.

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.

Tsadar Sadaki Na Sa Matasa Da Dama Gujewa Yin Aure – Shugaban Uganda Ya Gargadi Iyaye Su Rage Sadakin ‘Ya’yansu

Ku mutanen Banyankole kuna lalata ci gaban yawan jama'a. Iyaye, me ya sa kuke sayar da 'ya'yanku? Shanu 16, ban ma san adadin sauran ba. Me ya sa dole ne ku tara dukiya ta hanyar 'ya'yanku? Me ya sa ba za ku yi aiki ku sami abin ku da kanku ba?" in ji Museveni.

Kada A Rika Ba Jarirai Yan Ƙasa da Wata Shida Abinci Mai Tauri Kamar Tuwo, Koko, Kunu ko Fura – Likitocin Yara Sun Gargadi...

hakan na iya jefa su cikin haɗarin ƙarancin jini (anaemia), kamuwa da cututtuka da kuma shaƙewa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img