BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta bayan fitowarta daga gidan yari
Daga Wakiliya
Wani mutum mai shekaru 42 a Brazil, Gilberto Nogueira de Oliveira, ya ce yana shirin sake auren tsohuwar matarsa, Daiane dos Santos Farias, duk da cewa ta yanke masa azzakari da reza bayan ta gano ya ci amanarta.
Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Disamba, 2023, bayan Daiane ta gano cin amanar a ranar zagayowar haihuwarta.
Rahotanni sun ce Daiane ta yaudari mijin nata suka shiga jima’i, inda ta ɗaure hannayensa da wando, sannan ta yanke masa azzakari ta zubar da shi a bayan gida.
An yanke wa Daiane hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da watanni takwas a gidan yari, amma an sake ta kafin cikar wa’adin hukuncin a watan Nuwamba.
Bayan fitowarta, Gilberto ya sake tuntubarta domin su farfaɗo da soyayyarsu, yana mai cewa har yanzu yana sonta kuma ya yi kewarta.
Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.




