Amnesty ta nuna damuwa kan matsin lamba ga ’yan adawa a Kaduna

DA DUMI-DUMI

Amnesty ta nuna damuwa kan matsin lamba ga ’yan adawa a Kaduna

Daga Wakiliya

Kungiyar Amnesty International ta nuna damuwa kan abin da ta ce ƙara matsa lamba da ake yi wa masu sukar gwamnatin Kaduna da ’yan adawa a jihar.

Kungiyar ta ce masu sukar gwamnatin Gwamna Uba Sani na fuskantar barazanar kamawa da garkuwa da su, yayin da wasu ayyukan jam’iyyun adawa ke fuskantar hare-hare da wasu matakan da ta bayyana a matsayin danniya.

Amnesty ta ce hakan na haifar da yanayin tsoro da ka iya takura wa ’yancin faɗar albarkacin baki da na yin siyasa a jihar.

A cikin sanarwar, kungiyar ta ce sabon lamarin ya shafi Ibrahim Modibbo Sanusi, wanda ta ce an kama shi a daren Litinin 21 ga Satumba a Aruwa Plaza da ke Kaduna.

Ta kuma ambaci wani mazaunin Zariya, Isah Fresh, wanda ta ce an kama shi a farkon watan Satumba bayan wallafa wani bidiyo a kafar sada zumunta da ke sukar Gwamna Uba Sani.

Amnesty ta yi kira ga ’yan sandan Najeriya da su tabbatar da bin ƙa’idojin doka, tare da guje wa kamawa ko tsare mutane ba tare da bin ka’ida ba saboda ra’ayoyinsu na siyasa ko kuma abin da suka faɗa.

Kungiyar ta ce hukumomin tsaro bai kamata su zama kayan aikin ’yan siyasa ba, tana mai cewa ya kamata a mutunta ’yancin faɗar albarkacin baki, haɗuwa da jama’a da bayyana ra’ayi.

A wani saƙon da ya yi tsokaci kan rahoton Amnesty, an kuma yi kira ga Gwamna Uba Sani da ya tabbatar da cewa ’yan adawa na iya gudanar da harkokinsu na siyasa cikin ’yanci.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa Amnesty ta kuma soki wasu matakan ’yan sanda a Kaduna da suka shafi ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img