‘Ku bar Tinubu ya kammala wa’adinsa kada Yarabawa su juya mana baya’ – Shehu Sani ya gargadi Arewa

DA DUMI-DUMI

‘Ku bar Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekara 8 kada Yarabawa su juya mana baya’ – Shehu Sani ya gargadi Arewa

Daga Wakiliya

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya gargadi Arewa kan abin da ya kira ƙirƙirar abokan gaba da dama a siyasa, yana mai cewa hakan na iya jefa yankin cikin ƙarin masu adawa da ita.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a wata hira da ATP Hausa, inda ya ce bai kamata siyasar yau ta sa Arewa ta manta da tsohuwar alaƙarta da al’ummar Yarbawa ba.

Ya ce babu wani yanki ko ƙabila da za ta iya samun shugabancin Najeriya ita kaɗai, don haka ya kamata ‘yan siyasa su ƙarfafa kawancen da suke da shi maimakon ƙara yawan masu adawa da su.

Sanatan ya kuma yi kira ga ‘yan Arewa da su bar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kammala wa’adinta na shekaru huɗu cikin kwanciyar hankali, (ya yi shekara 8) yana mai gargadin cewa duk wani yunƙurin kwace mulki da ƙarfi zai iya haifar da rashin zaman lafiya.

Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli da rashin fahimta da wasu yankuna da ƙabilu, don haka bai kamata ta ƙara jawo wa kanta rikici da Yarbawa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img