‘Ku zo ku kama ni idan kun isa’ – Alkali Askira ya shiga ‘Tinubu Must Go’
Daga Wakiliya
Wani lauya kuma mai fafutuka daga jihar Borno, Barrista Alkali Adamu Askira, ya sanar da shiga gangamin ‘Tinubu Must Go’, bayan an kama wasu matasa biyar a Maiduguri bisa zargin sanya T-shirt mai dauke da taken.
Askira ya ce abin da ya faru ya zama abin kunya da kuma barazana ga dimokuraɗiyya.
Ya ce saboda haka ya dakatar da tafiyar One-Time President (OTP) da yake jagoranta, tare da bayyana cewa zai shiga gangamin ‘Tinubu Must Go’.
“Daga yau, ni Alkali Adamu Askira, da kaina na shiga wannan tafiya. Ku zo ku kama ni idan kun isa,” in ji shi.
Matasa biyar da aka ce an kama a West End Roundabout, su ne Baba Aji Gremami, Mustapha Abba Yemen, Abacha Mohammed Ali, Adam Umar Gubio da Abdulhamid Mohammed.
Askira ya kuma yi kira ga gwamnatin Borno da ta yi amfani da ofishin Antoni Janar na jihar wajen ganin an saki matasan, idan ba ta da hannu a kama su.




